Dalilan da ke sa Malamai da fasto-fasto yin ‘fyade’ a wurin ibada | BBC Hausa

Zargin fyade
Image caption

Masu zanga-zanga na cewa ‘Fastonka ba Ubangijinka ba ne’

A har kullum a kan samu yanayin da jagororin addini kan aikata wasu laifuka a matsayinsu na mutane. To sai dai kasancewar su jagorori a addini ya sa jama’a ke mamaki da shiga dimuwa idan mutanen da suka amince da su suka yi ba zata.

Batun yi wa mata musamman kananan yara da matasa fyade wani abu ne da ke ci gaba da ruruwa kamar wutar daji, inda a lokuta da dama a kan samu jagororin addini a irin wannan matsala.

Kwararru kan masu tabin hankali irin su Dakta Babagana Kundi Machina, Shugaban Asibitin Kwararru na jihar Yobe da ke birnin Damaturu, sun zayyana wasu dalilai guda biyu da suka ce su ne ke sa jagororin addini yin fyade.

  • Irin yardar da ke tsakanin fasto-fasto ko malamai da mabiyansu da ke sa har su kebe musamman mata
  • Rashin fallasa matsalar fyade idan ta faru
  • Da kuma rashin hukunta wadanda aka samu da laifin aikata fyaden
  • Zanga-zangar kyamar ‘fyade’ da ake zargin Fasto da yi
  • Kalli yadda aka yi zanga-zanga kan fyade a Coci

Tasirin fyade a kan wadanda aka yi wa

Dakta Babagana Kundi Machina ya ce mafi yawancin lokaci wadanda aka yi wa fyade musamman mata kan fuskanci wasu matsaloli kamar haka:

  • Yiwuwar samun matsaloli dangane da nutsuwarta da kimarta
  • Zai shafi tunaninta, abin da zai sa mata ciwon damuwa
  • Samun rashin kauna ko son kasancewa da namiji

Illar Fyade a cikin al’umma

  • Mutane za su iya daukar doka a hannunsu
  • Za a iya samun magoya bayan jagoran addini yin fito na fito da masu zargin sa
  • Za a iya samun mutanen da ka iya fita daga addini kasancewar

Ya ya za a magance matsalar?

Dakta Babagana ya bayar da shawarwari da ya kira matakan kariya kamar haka:

  • Wayar da kan yara dangane da abubuwan da ya kamata su kiyaye kamar illar taba musu al’aura
  • Iyaye su ja ‘ya’yansu a jika domin samun natsuwar yi musu bayani idan wani abu ya same su
  • hukunta masu laifi domin ya zama izna ga masu son aikata irin wannan laifi

A karshen makonnan ne dai gomman masu fafutuka suka gudanar da zanga-zanga a Abuja da Legas na Najeriya da manufar bayyana wa mutane irin barnar da wasu fasto-fasto ke yi a majami’u.

An dai gudanar da zanga-zangar ne da manufar nema wa wata wadda ta yi zargin faston cocin Commonwealth of Zion Assembly COZA, Pastor Biodun Fatoyinbo da yi mata fyade.

To sai dai yayin da masu zanga-zangar ke kokarin goyon bayan Bisola Dakolo, a gefe guda an samu wasu masu zanga-zangar da ke goyon bayan Fasto Biodun Fatoyinbo.

Me Bisola take zargin Fasto da shi?

Image caption

Bisola mai dakin fitaccen mawakin nan ne Timi Dakolo

Bisola Dakolo dai ta fito a wani bidiyo inda ta yi hira da wani dan jarida take sheda masa cewa Fasto Biodun ya yi mata fyade lokacin tana ‘yar shekara 16.

Ta kara da cewa ya yi mata fyaden ne fiye da sau daya, inda a karon farko faston ya yi lalata da ita a cikin gidansu da misalin karfe shida na safe.

Da aka tambaye ta dalilin da ya sa ba ta yi ihu ba domin jama’a su kai mata dauki sai ta ce “Ya rufe min baki.”

Bisola dai yanzu haka mai dakin fitaccen mawakin nan ce, Timi Dakolo kuma tana da yara.

Mene ne martanin fasto?

Image caption

Fasto Biodun ya ce ana son bata masa suna

Kwatsam bayan kammala ibadar ranar Lahadi, sai Fasto Biodun ya fito ya yi wa mahalarta cocin na sa jan kunne cewa ka da su shiga rikici saboda zargin lalata mata.

Ya kara da yin kira ga magoya baya da su zama masu zaman lafiya ka da su tayar da zaune tsaye.

Sai dai a wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a, faston ya ce sam bai taba yi wa wata mace fyade ba, inda ya yi barazanar kai Bisola gaban kuliya.

Ya kuma danganta ikirarin da wani yunkurin bata sunansa da na cocin.

More News

Yawan Mutanen Da Suka Mutu A Wutar Da Wani Matashi Ya Cinnawa Wani Masallaci A Kano Sun  Karu Zuwa 16

Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta ce yawan mutanen da suka mutu sakamakon wutar da wani ya cinnawa wani masallaci a ƙauyen Gadan a...

An fara rushe wasu gine-gine 500 a kasuwar Karmo dake Abuja

Hukumar FCTA dake kula da birnin tarayya Abuja ta fara rushe gine-gine sama da 500 da aka yi ba bisa ka'ida ba a kasuwar...

Tinubu ya tarbi shugaban kasar Senegal Bassirou Faye a fadar Aso Rock Villa

A ranar Alhamis ne shugaba Bola Tinubu ya tarbi shugaban kasar Senegal Bassirou Faye a fadar Aso Rock Villa, a ziyarar da Faye ya...

NEMA ta karɓi ƴan Najeriya 150 da aka dawo dasu gida daga ƙasar Chad

Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Ƙasa NEMA ta ce ta karɓi ƴan Najeriya 150 da aka dawo da su bayan da su ka maƙale...