Dalilai biyar da suka ramar da jaridun Najeriya sosai | BBC Hausa

  • Awwal Ahmad Janyau
  • BBC Abuja

Yadda jaridun Najeriya suka rame abin tambaya ne – Ko da yake ana cewa rama ba mutuwa ba.

Yawanci jaridu masu zaman kansu a Najeriya sun saba fitowa ƙunshe da shafuka kusan 60 ko fiye, amma shafukan jaridun da ake buga wa kamar Daily Trust da Punch da Leadership da ThisDay da sauransu ba su wuce shafi 35 ba a yanzu.

Ramewar jaridun ta nuna abubuwa sun sauya, kuma masana na ganin tun kafin annobar korona jaridun Najeriya suka fara shiga matsala da ta tilasta rage yawan shafukan da suka saba bugawa.

Abdurrahman Abubakar, tsohon É—an jarida a Daily Trust, ya shaida wa BBC dalilai biyar da yake ganin sun yi tasiri wajen ramewar jaridun na Najeriya.

Kafofin watsa labarai na Intanet

Jaridun intanet yanzu sun shahara sosai musamman saboda bunkasar amfani da intanet a Najeriya.

Jaridun intanet suna cikin manyan shafukan intanet da aka fi ziyarta a Najeriya. Kuma saboda wadatuwar wayoyin salula musamman na zamani, Æ´an Najeriya sun koma dogaro da intanet wajen samun labarai.

Samuwarsu ya sawwake samun labarai cikin lokaci – da za a iya yaÉ—awa nan take inda suka danne hanyoyin da a al’adance aka saba samun labarai kamar jaridu da gidajen rediyo da talabijin.

Abdurahman ya ce kafofin watsa labarai na intanet sun yi tasiri sosai ga ƙalubalen da jaridu ke fuskanta, duk da yake suna da nasu shafukan na intanet.

Mutane sun samu hanyoyi da dama na intanet na samun labarai, kuma tun daga wannan lokacin jaridu suka fara samun matsala – domin labaransu ba su saurin kai wa ga mutane.

“Tun kafin korona wannan ya shafe su ta yadda mutane da yawa sun daina dogaro da su kuma suka daina sayen jaridun, suka koma dogaro da kafofin rediyo da kuma masu watsa labarai a intanet.

Yawanci yanzu labaran da mutane suka riga suka sani ne jaridun ke buga wa, wanda kuma ya yi tasiri ga raguwar sayen jaridun.

A baya jaridu na cin karensu ba babbaka – babu intanet sai sun fitar da labari ake sani ko da kuwa kafin fitowar jaridar abin ya faru.

Annobar Korona

Annobar korona ta yi illa sosai ga gidajen jaridu a Najeriya, kuma wannan na daga cikin manyan dalilin da ya ramar da jaridun.

Yawanci jaridu a Najeriya sun dogara ne kan abubuwan da ke faruwa a gwamnatance da abubuwan da ke faruwa a tsakanin jama’a ta fuskar samun labarai.

Amma lokacin kullen korona labaru sun yi wahala – komi ya tsaya cak kuma ba wani labari sai labarin korona. Jaridu ba za su zuba duk labaran korona a shafi 40 ba na jaridunsu.

Korona ta yi illa ga karfin tattalin arzikin mutane da gwamnatocin kasashe – inda aka yi watanni cikin dokar kulle, matakin da ya shafi ko wane É“angare na tattalin arziki.

Wahalar samun kuÉ—i ga mutane na yau da kullum ya sa waÉ—anda ke hakurin sayen jaridun sun koma dogaro da kafofin watsa labarai na intanet da suke samu ba tare da biyan kudi ba domin samun labarai.

Ofisoshin gwamnatoci da na kamfanoni masu zaman kansu sun kasance a rufe saboda kullen korona waÉ—anda ke sayen jaridun da kuma bayar da tallace-tallace.

Annobar korona ta haifar da wahalar samun kuÉ—aÉ—en kasashe waje domin sayen kayan aiki, sannan canji ya yi tsada inda gidajen jaridun ke shan wahala wajen samun canjin.

Abdurrahman ya ce gidajen jaridun sun ga cewa da suka riƙa buga jaridun da ba a saya kuma suna shan wahala wajen samun kudi gara su rage yawan shafukan da suke bugawa don su rage hasara.

Fatarar Tallace-Tallace

Yawancin jaridun Najeriya sun dogaro ne kacokan ga tallace-tallace da suke samu daga gwamnati da kamfanoni da masu iko da Æ´an kasuwa.

Kusan babu jaridar da za ta ce tana dogaro da kudaden da mutane ke sayen jarida naira 200 zuwa naira 250 – idan kuma haka ne ba za ta kai labari ba.

Tallace-tallacen da jaridun ke samun kudi ta hanyarsu sun ja baya a yanzu saboda akwai lokacin da jaridun suka fi samun tallace-tallacen a Najeriya.

An fi samun talla lokacin siyasa – yanayin da ake ciki yanzu ya taimaka wajen ramar da jaridun da har suka koma buga shafi 30 zuwa 40 a yanzu.

Annobar korona da ta shafi harakokin gwamnati ta yi tasiri ga rashin samun tallace-tallacen ga jaridun Najeriya, saboda gwamnati ta zabtare abubuwa da yawa na harakokin da suka shafe ta.

Haka kuma mutane da jami’an gwamnati da Æ´an kasuwa da ke ba jaridu talla kamar na taya murnar zagayowar murnar haihuwa duk sun ragu.

Tashin dala

Tun farkon fara sarrafa jarida har zuwa fitowarta kusan kashi 85 cikin 100 na kayan aikin daga kasar waje ake shigo da su – tun daga kwamfuta da tawada da takardar buga jarida da kayan gyaran mashin buga jaridar kuma babu wani rangwame da gwamnati ta ke yi wa jaridun na harajin shigowa da kayan.

Tashin farashin dala ya ƙara wa aikin buga jarida tsada.

Dole jaridun su rage yawan shafukan da suke buga wa saboda gaba É—aya ana buga shafukan ne ba don riba ba. Idan jarida ta ce za ta buga shafuka da yawa za ta yi hasara domin kayan buga jaridar sun kara tsada.

Ana ganin wannan dalilan ne ya sa wasu jaridun ke datse yawan ma’aikatansu – domin jarida kasuwanci ne saboda kuÉ—in da ke shigowa gidajen jaridun ya yi kasa sosai.

Wasu sun mayar da ma’aikatan na wuccin gadi bisa yawan labaran da suka bayar.

Rashin binciken labarai na musamman

Yawancin labaran da yanzu da jaridun Najeriya ke buga wa, mutane sun riga sun san da su ta hanyar kafofin watsa labarai na intanet da kafofin sadarwa.

Amma tanadin labarai na musamman ga jaridu suna taimakawa ga janyo hankalin mutane kuma a lokacin da labarai suka yi wahala.

Sai dai irin waÉ—annan labaran ba haka kawai suke zuwa ba, labarai ne masu tsada masu bukatar bincike sosai kafin a kammala haÉ—a su.

Yawanci jaridun Najeriya suna shan wahala wajen samun irin waÉ—annan labarai nasu na musamman da suka samo saboda sun fi dogaro da abubuwan da ke faruwa a gwamnatance da kuma waÉ—anda ke faruwa tsakanin al’umma

Kamar a mako É—aya da ake buga jarida sau bakwai da Æ™yar jarida ke iya samun labarinta na kanta da ta yi bincike akai – dole sai dai ta dogara da labaran al’umma na yau da kullum wadanda kuma za a iya samu a dukkanin jaridun.

Wasu labaran da za ku so ku karanta

Me ya kamata jaridun Najeriya su yi

Ganin yadda jaridun Najeriya ke gogayya da na intanet, ya kamata su faÉ—aÉ—a bincike – su mayar da hankali ga bayar da labari na bincike wadanda suka bincika da kansu.

Labarai na musamman nasu na kansu zai taimaka masu sosai, saboda mutanen da ke karanta labaran ya kasance suna da sabon labari da ba su sani ba wanda za su karanta. Duk abin ba da ba su ji ba ya kasance za su samu a jaridu.

Mayar da hankali kan labaran da suka shafi jama’a kai tsaye wanda zai janyo hankalinsu, shi ma zai taimaka – zai sa mutane su iya sayen jaridar.

Sai sun faÉ—aÉ—a harakokin jarida sun tafi da zamani – yanzu jarida ta sauya kowa yana shiga aikin kowa tsakanin gidan talabijin da rediyo da gidan jarida.

Ya kamata jaridun su kasance suna ko ina, duk labarin da ake nema suna da shi har a shafukan sada zumunta na intanet.

More News

Gwamnan Kano ya sanya hannu kan dokar yin gwajin lafiya kafin aure

Gwamnan jihar Kano, Engr Abba Kabir Yusuf ya sanya hannu kan wata doka za ta tilastawa masu yin aure yin wasu gwaje-gwajen lafiya gabanin...

An kashe kwamandan soji a Katsina

An kashe kwamandan sojoji na wani sansanin soji da ke Sabon Garin Dan’Ali a karamar hukumar Danmusa a jihar Katsina a wani harin kwantan...

Magoya bayan APC da dama sun koma NNPP a Kano

Jam'iyar NNPP ta karɓi magoya bayan jam'iyar APC da dama a jihar Kano. Mataimakin gwamnan jihar Kano, Aminu Abdul Salam Gwarzo shi ne ya karɓi...

APC ta dakatar da Ganduje a matakin gunduma

Mambobin jam'iyyar APC a mazabar da ke Karamar Hukumar Dawakin Tofa a Jihar Kano sun dakatar da Shugaban Jam’iyyar APC na kasa Abdullahi Ganduje. ...