Dalilai biyar da kasashen Yamma suka damu da Saudiyya

Tutar Saudiyya a gaban karamin ofishin jakadancin kasar Turkiya da ke birnin Santanbul, ranar 13 ga watan Oktoba 2018

Saudiyya ta zama kasa mai muhimmanci a fannin tattalin arziki da siyasa

Shugaban Amurka Donald Trump ya yi barazanar daukar tsattauran matakin ladabtarwa a kan Saudiyya, idan har ta tabbata cewa ita ce ta kashe fitaccen dan jarida Jamal Khashoggi.

Dan jaridan Saudiyyar wanda ya bace tun bayan da ya ziyarci karamin ofishin jakadancin kasar a babban birnin Turkiyya, Santanbul.

Saudiyyar wadda ta yi watsi da zargin da jami’an Turkiyya suka yi mata na cewa jami’an Saudiyyar ne suka halaka shi, ta lashi takobin mayar da kakkausan martani ga duk wani tsattsauran mataki da kasashen Yammacin duniya za su dauka a kanta.

Me wannan dambarwa za ta iya haifarwa?

1. Samar da mai da farashinsa

Saudi Arabia ce take da kusan kashi 18 cikin dari na arzikin mai da aka tabbatar a duniya, kuma ita ce kasa ta daya da ta fi sayar wa kasashen duniya man, kamar yadda kungiyar kasashe masu arzikin mai ta duniya (Opec) ta bayyana.

Wannan ne ya ba wa kasar ta Saudiyya karfi da kuma tasiri a tsakanin kasaashen duniya.


Yarima Mohammed ya ce yana son Saudi Arabia ta rage dogaro a kan arzikin mai

Idan a misali Amurka ko wata kasa ta sanya wa Saudiyya takunkumi, gwamnatin Saudiyyar za ta iya mayar da martani ta hanyar rage yawan man da take samarwa, wanda hakan zai iya sa farashin man ya tashi, muddin wasu kasashen ba su cike wannan gibi ba.

A wani sharhi da aka wallafa ranar Lahadi, shugaban tashar talabijin ta Al Arabiya TV mallakar Saudiyyar, Turki Aldakhil ya ce sanya wa kasar takunkumi zai haifar da bala’in tattalin arziki da zai girgiza duniya.

A sharhin ya kara da cewa: “Idan har tashin farashin mai zuwa dala 80 ya bata wa Shugaba Trump rai, ba wanda zai ce farashin ba zai iya kaiwa dala 100 ba, ko ma dala 200, ko kuma ma ya linka wannan farashin biyu ba.”

Sai dai duk wani karin farashi zai kare ne ga masu amfani da man, ta yadda za a kara farashinsa a gidajen mai.

2. Kwantiragin soji

A shekara ta 2017 Saudi Arabia ce ta uku a girman kasafin tsaro a duniya, kamar yadda bayanan cibiyar bincike kan zaman lafiya ta duniya, Stockholm International Peace Research Institute (Sipri) suka nuna.

A wannan shekara kasar ta kulla yarjejeniyar sayen makamakai ta dala biliyan 110 da Amurka, da wata karin dama ta kara yarjejeniyar ta kai har ta dala biliyan 350 a tsawon shekara 10.

Fadar gwamnatin Amurka, White House, ta bayyana yarjejeniyar da cewa ita ce daya mafi girma a tarihin Amurkar.

Sauran wasu kasashen da ke sayar wa Saudiyya makamai sun hada da Birtaniya da Faransa da Jamus.

Sharhin Aldakhil ya nuna cewa wannan ma wani bangare ne da gwamnatin Saudiyya za ta iya mayar da martani a kan duk wani takunkumi da kasashen Yamma za su iya sanya mata, ta yadda za ta karkata ga China da Rasha wajen neman biyan bukatunta na soji.

3. Tsaro da ta’addanci

Kasashen Yammacin duniya sun jaddada cewa Saudi Arabia tana taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da tsaro a Gabas ta Tsakiya, tare da kawar da tsattsauran ra’ayi da ta’addanci.

Fira ministar Birtaniya Theresa May ta nuna muhimmancin ci gaba da alaka ta kut da kut da Saudi Arabia duk da yadda ake zargin sojinta da aikata laifukan yaki a rikicin Yemen, inda ta kafe cewa Saudiyyar ta taimaka wajen tabbatar da tsaron lafiyar jama’a a titunan Birtaniya.


Shugaban Amurka Donald Trump ya halarci taron bude cibiyar yaki da tsattsauran ra’ayi a Riyadh a 2017

Kasar wadda ita ce cibiyar Musulunci, mamba ce a cikin kasashen da suka yi taron-dangin da Amurka ke jagoranta wajen yaki da kungiyar IS.

Kuma a shekarar da ta wuce ne ta kirkiro wata hadakar kasashe 40 na Musulmi domin yaki da ta’addanci, hadakar da aka sanya wa suna da Islamic Military Counter Terrorism Coalition.

Aldakhil ya kuma yi hasashen cewa batun musayar bayanai tsakanin Saudiyya da Amurka zai zama abin tarihi, wato za a daina shi idan har aka dauki wani mataki a kan kasar a game da batan Khashoggi.

4. Hadin kai a yankin

Saudi Arabia ta yi aiki kut da kut tare da Amurka domin hana Iran tasiri a yankin na Gabas ta Tsakiya.

Kasashen Musulmin masu bin akidar ‘yan Sunni da kuma ‘yan Shia suna rikici da juna a fakaice a fadin yankin na Gabas ta Tsakiya tsawon shekara da shekaru.

A Syria, Saudi Arabia ta mara baya ga bangaren ‘yan tawayen da ke kokarin hambarar da Shugaba Bashar al-Assad, yayin da ita kuma Iran da hadin guiwar Rasha ke taimaka wa Shugaban.

A sharhin labaransa, Aldakhil ya yi gargadin cewa kyautatuwar dangantaka tsakanin Saudi Arabia da Rasha a sanadiyyar takunkumin Amurka, da kuma kulla wata sabuwar yarjejeniyar makamai da Moscow, ka iya kaiwa ga kusanci da Iran har ma ya iya kaiwa ga sasantawa da ita.

5. Kasuwanci da zuba jari

Janar manajan na tashar talabijin din ta Al Arabiya ta Saudiyya ya kuma ce lamarin zai iya kaiwa ga hana kamfanonin Amurka shiga kasuwar Saudiyya.

Cinikayyar kayayyaki da ayyuka da ke tsakanin Amurka da Saudiyya ta kai ta jumullar dala biliyan 46 a shekara ta 2017, inda Amurkar ta samu rarar kasuwancin da ta kai ta dala biliyan biyar.

Ma’aikatar kasuwanci ta Amurka ta yi kiyasin cewa huldar kasuwancin da ke tsakanin kasashen biyu ta taimaka wa guraban aiki kusan dubu 165 a Amurka a shekara ta 2015.

A watan Agusta, Saudi Arabia ta dakatar da dukkanin sabbin yarjeniyoyin kasuwanci da ta kulla da Canada saboda abin da ta kira tsoma baki a harkokinta na cikin gida, inda ta bayyana kiran da gwamnatin Canada ta yi kan ta saki masu rajin kare hakkin dan adam da ‘yancin mata da ta tsare a matsayin keta haddin ‘yancin Saudiyyar.

Gwamnatin Saudiyyar ta kuma dakatar da sayo alkama da sauran nau’in hatsi daga Canada sannan kuma ta dawo da dubban ‘yan kasarta da ta ba wa tallafin karatu a jami’o’in kasar ta Arewacin Amurka.

More News

Kwankwaso ya bada tallafin miliyan ₦50 ga mutanen da ambaliyar Borno ta shafa

Tsohon gwamnan jihar Kano kuma jagoran jam'iyar NNPP, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya bada tallafin naira miliyan 50 ga mutanen da ambaliyar ruwa a...

Sakamakon NECOn 2024 ya fito

Hukumar shirya jarabawar ta kasa ta fitar da sakamakon jarabawar kammala sakandare ta watan Yuni/Yuli 2024, inda kashi 60.55 cikin 100 na waÉ—anda suka...

Ƴan Najeriya na shan baƙar wahala—Janar Abdulsalami

Tsohon shugaban kasa, Janar Abdulsalami Abubakar, ya ce wahalhalun da ake fama da su a Najeriya na kara tabarbarewa, kuma rabon kayan agajin ba...

EFCC ta musalta cewa Yahaya Bello na tsare a ofishin hukumar

Hukumar EFCC dake yaƙi da masu yiwa tattalin arzikin ƙasa ta'annati ta ce tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello baya ya tsare a hannunta. A...