
Mikel Arteta
Dan wasan gaban Borussia Dortmund Jadon Sancho baya tunanin inda zai koma, duk da alakanta shi da komawa Manchester United ko Liverpool.(Mail).
Tottenham za ta nemi mai tsaron ragar Watford Ben Foster wanda yarjejeniyarsa da kungiyar za ta kare bana.(Sun).
Hakama Tottenham din na fatar ganin ta shiga gaban Roma wurin sayen mai tsaron bayan Manchester United Chris Smalling.
Yanzu haka Smalling mai shekaru 30 na zaman aro a Roma.(Calciomercato, in Italian).
Hakkin mallakar hoto
Getty Images
Smalling na zaman aro a Roma
Manchester United na sahun gaba cikin masu son sayen mai tsaron bayan Napoli na Italiya Kalidou Koulibaly.
Kungiyoyin Real Madrid da PSG hakama na neman dan kasar Senegal din mai shekaru 26.(Express, via Corriere dello Sport).
Mai horar da kungiyar Arsenal Mikel Arteta ba zai samu kudi mai yawa ba wurin sayen yan wasa, matsawar kungiyar ta kasa zuwa gasar zakarun turai a badi.
Rahotanni na cewa Arsenal ta kasa samun ribar azo a gani a bana.(Goal).
Shugaban kungiyar Inter Milan Giuseppe Moratta na tunanin ba za’a kammala kakar wasannin bana ba, in har ba’a samu mafita ba kan yaduwar cutar Coronavirus.
Mai horar da Manchester City Pep Guardiola ya ce ba za a iya ja da kungiyarsa ba idan ana maganar lashe kofunan cikin gida.
Hakan na zuwa bayan kammala wasan karshe na kofin Carabao inda City ta doke Aston Villa da ci 2-1 a filin Wembley. (BBC).