DA ƊUMI-ƊUMI: Kungiyoyin ƙwadago za su tsunduma yajin aiki ranar Litinin

Mambobin kungiyar kwadago, a ranar Juma’a, sun shelanta yajin aikin sai baba-ta-gani a fadin kasar saboda kin amincewar da gwamnatin tarayya ta yi na kara karin mafi karancin albashi daga N60,000.

Shugaban kungiyar kwadago ta Najeriya Joe Ajaero ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai da ke gudana a gidan ma’aikata dake Abuja.

Ajaero ya ce za a fara yajin aikin ne da tsakar daren ranar Lahadi 2 ga watan Yuni, 2024.

A ranar Juma’ar ne dai tattaunawa kan batun mafi karancin albashi tsakanin Gwamnatin Tarayya da kungiyoyin kwadago ta lalace a lokacin da gwamnatin ta kasa sauya sheka kan N60,000 da ta gabatar a taron da ya gabata.

More from this stream

Recomended