A ranar Laraba ne gwamnatin jihar Bauchi ta tabbatar da bullar cutar maƙogoro da yellow fever a jihar.
Da yake tabbatar da bullar cutar, Babban Sakataren Hukumar Kula da Lafiya a matakin farko ta Jihar Bauchi (BSPHCD), Dokta Rilwanu Mohammed, ya ce daga cikin mutane 58 da ake zargin sun kamu da cutar, uku sun dawo lafiya, yayin da biyu kuma suka mutu sakamakon kamuwa da cutar.
Diphtheria cuta ce mai saurin yaduwa wanda ke haifar da kumburin cikin hanci da baki da samuwar fatar da ba ainihin wajen zamanta ba ke nan a cikin makogwaro, tare da hana numfashi da hadiya.