
Hakkin mallakar hoto
Getty Images
Sakataren kasuwanci na Amurka Wilbur Ross ya ce annobar coronavirus a China na iya zama ci gaba ga tattalin arzikin Amurka.
Yayin wata hira da wani gidan talabijin Mista Ross ya ce: “Ina tunanin za ta taimaka matuka wajen hanzarta dawo da ayyukan yi zuwa Arewacin Amurka”.
Bazuwar coronavirus ta sanya fargaba game da tasirin cutar ga tattalin arzikin China da kuma ci gaban duniya.
Wadannan kalaman sun fuskanci suka daga masu adawa da gwamnatin Shugaba Trump.
Da yake amsa wata tambaya kan ko barkewar cutar hadari ne ga tattalin arzikin Amurka, Mista Ross ya ce: “Ba na son magana game da samun nasara kan mummunar cuta.”
Daga bisani, ma’aikatar kasuwancin Amurka ta sake jaddada kalamansa: “Kamar yadda Sakatare Ross ya fada, mataki na farko shi ne dakile bazuwar cutar sannan a taimaka wa wadanda suka kamu da ita.”
“Yana da mahimmanci a duba illar yin kasuwanci da kasar da take da dadadden tarihin boye hadarurruka ga al’ummarta da kuma duniya baki daya,” a cewarsa.
An caccaki kalaman inda dan majalisa daga jam’iyyar Democrat Don Bayer ya shiga shafin Twitter domin kalubalantar batun gano ribar kasuwanci yayin da ake fama da annobar.
Masana tattalin arziki su ma sun kalubalanci kalaman na Mista Ross. Simon Baptist na sashen kula da bayanan sirri na tattalin arziki a Singapore ya shaida wa BBC cewa kalaman na Ross sun yi matukar ba shi “mamaki”.
“Kamfanoni ba za su dauki wasu matakan zuba jari ba kan barkewar wata cuta da ka iya shafe tsawon wata uku zuwa shida ana fama da ita,” a cewarsa.
Ya ce akwai yiwuwar kwayar cutar za ta iya yin mummunan tasiri ga Amurka maimakon samun ci gaba: “A zahiri, Amurka za ta yi babbar asara saboda ko da komai, China har yanzu babbar abokiyar kasuwancin Amurka ce, idan kuma tattalin arzikin China ya fuskanci koma baya hakan zai iya shafar Amurka. ”