Cutar coronavirus ta kashe mutum biyu a Iran | BBC Hausa

File photo showing people walking past the shrine of Fatima Masumeh in Qom, Iran (9 February 2020)

Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Qom is the location of the shrine of Hazrate Masoumeh, a revered female saint in Shia Islam

Ma’aikatar lafiya ta Iran ta ce mutane biyu sun mutu bayan gwajin da aka gudanar ya tabbatar suna dauke da cutar coronavirus.

Kuma hukumomi sun ce cutar ta yi saurin kashe su ne saboda manyan shekarunsu a yayin da suke jinya a asibitin Qom.

Mataimakin Ministan lafiya na Iran Qasem Janbabaei ya shaida wa kungiyar matasan ‘yan jarida ta YJC cewa dukkaninsu Iraniyawa ne.

Su ne mutane na farko da aka tabbatar da sun mutu sakamakon kamuwa da cutar Coronavirus a Iran.

Kamfanin dillacin labaru na Iran IRNA ya ruwaito cewa mutanen ba su tafi kasashen waje ba ko fita daga lardin Qom kafin rasuwarsu.

Daga baya kuma kamfanin dillacin labaran ya ce za a rufe makarantu da jami’oi a lardin ranar Alhamis, a wani mataki na dakile yaduwar cutar.

An ruwaito Mista Janbabaei na cewa zuwa yanzu babu wanda ke dauke da cutar a wajen Qom.

Amma BBC ta fahimci cewa mutum 25 aka killace a asibitin Qom wadanda ake tunanin suna dauke da cutar Covid-19.

Sauran kasashen da coronavirus ta bulla

A Gabas ta Tsakiya, Kasar Daular Larabawa ta tattabar da mutum tara da ke dauke da cutar – dukkaninsu ‘yan asalin China – amma zuwa yanzu babu wanda ya mutu.

A Masar, wani dan kasar waje da aka tabbatar yana dauke da cutar an bayyana cewa yanzu yana samun sauki bayan amfani da sabon gwajin maganin cutar wanda ya nuna cewa ba shi dauke da cutar.

Amma zai ci gaba da zama a killace har sai bayan mako biyu.

Tun a ranar Talata, Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta ce mutum 75,197 aka ruwaito suna dauke da Covid-19 kuma 2009 suka mutu. Kuma a China ne cutar ta fi yin kisa inda ta fi yin kamari.

Sai dai kuma babban jami’in Hukumar Lafiya ta Duniya WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus ya shaidawa taron manema labarai cewa alkalumman da ake samu a China a yanzu na raguwa.

More from this stream

Recomended