A ranar Litinin ne gwamnatin tarayya ta tabbatar da bullar cutar anthrax a Najeriya, inda ta bayyana cewa an gano cutar a wata gona da ke jihar Neja.
A ranar 13 ga watan Yuni, 2023, jaridar PUNCH ta ruwaito cewa, gwamnatin tarayya ta sanar da jama’a game da barkewar cutar anthrax a wasu kasashen da ke makwabtaka da yankin Afirka ta Yamma, ta kuma shawarci ‘yan Najeriya da su daina cin ganda, wanda aka fi sani da ponmo.
Gwamnatin kasar ta bayyana musamman cewa cutar ta yadu a arewacin Ghana mai iyaka da Burkina Faso da Togo, kamar yadda ta kuma yi alkawarin ci gaba da sanar da ‘yan Najeriya bayanai game da cutar.
A cikin wata sanarwa da ma’aikatar noma da raya karkara ta tarayya ta fitar a Abuja ranar Litinin, ta ce ta damu matuka da sanar da tabbatar da bullar cutar anthrax a jihar Neja ta Najeriya.