Cristiano Ronaldo ya ci kwallo na 136 a Champions League

Champions League

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,
Cristiano ya ci kwallo na 136 a Champions League shine kan gaba a zura kwallaye a gasar

Cristiano Ronaldo ya ci kwallo na 136 a gasar Champions League a wasan da Young Boys ta ci Mancheter United 2-1 ranar Talata.

Ronaldo ne ya fara cin kwallo minti 13 da fara tamaula, inda Young Boys ta farke ta hannun Nicolas Moumi Ngamaleu a wasan na rukuni na shida.

Daf da za a tashi Young Boys ta kara na biyu ta hannun Jordan Siebatcheu da hakan ya sa ta hada maki uku a karawar.

A wasa 68 da ya buga a Champions League tun bayan da ya cika shekara 30 da haihuwa, Ronaldo ya ci kwallo 63, jumulla yana da 136 a raga.

Hakan ya sa yana kan gaba da tazarar 35 tsakanin ‘yan wasan da suka kai shekara 30 ko fiye da haka da suka ci kwallo a tarihin Champions League.

Lionel Messi dan kwallon Paris St Germain shine na biyu a yawan cin kwallaye a Champions League mai 120 a raga.

United ta karasa karawar da ‘yan kwallo 10 a cikin fili, bayan da aka bai wa Wan Bissaka jan kati.

Aaron Wan-Bissaka shine dan wasan Manchester United na farko da aka bai wa jan kati a Champions League tun bayan wanda aka kori Nani a fafatawa da Real Madrid cikin Maris din 2013.

An buga karawar da ‘yan kallo a karon farko a gasar tun bayan 2020, sakamakon bullar cutar korona.

More News

Yahaya Bello Ya Bayyana Dalilan Da Ya Hana Shi Bayyana A Gaban Kotu

Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya ce tsoron kamun  hukumar EFCC dake yaÆ™i da yiwa tattalin arzikin Æ™asa ne ya hana shi bayyana...

Ƴan sanda sun kama mutane biyu dake samarwa ƴan fashin daji makamai a jihar Kaduna

Rundunar Æ´an sandan jihar Kaduna ta ce tana tsare da wasu mutane biyu da ake zargi da safarar bindiga a jihar. A wata sanarwa ranar...

An kori sojojin Najeriya biyu saboda satar kebul a matatar Dangote

Rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da korar wasu sojoji biyu da ake zargi da satar igiyoyin sulke a harabar matatar Dangote da ke jihar...

Magoya bayan APC da dama sun koma NNPP a Kano

Jam'iyar NNPP ta karɓi magoya bayan jam'iyar APC da dama a jihar Kano. Mataimakin gwamnan jihar Kano, Aminu Abdul Salam Gwarzo shi ne ya karɓi...