Covid- 19: An rage cin kasuwa a Najeriya—BBC News

Kasuwa

Jama’a da dama sun yi kaura da zuwa cin kasuwa a Najeriya saboda fargabar kamuwa da cutar coronavirus.

Bisa al’ada dai akwai wasu kasuwanni a Najeriyar da suke ci a wasu ranaku da aka kebe inda za a ga jama’a ba ma daga jihar da kasuwar ke ci ba, wani lokaci har daga makwabtan jihohi ana zuwa cin kasuwa.

BBC ta kai ziyara daya daga cikin irin wadannan kasuwanni da suke ci inda ta je kasuwar babbar kasuwar Suleja da ke jihar Neja domin ganin halin da ake ciki a kasuwar dama yadda kasuwar ke ci.

Ita dai wannan kasuwa ta na ci ne a duk ranakun Lahadi, kuma jama’a daga sassa da dama ne ke zuwa cin wannan kasuwa.

Ko da BBC ta isa wannan kasuwa ta tarar ba kamar ko yaushe ba, domin ba bu jama’a sosai.

To ko me ya jawo hakan? BBC ta tambayi shugaban ‘yan kasuwar Yakubu Yusuf Bagobiri.

Malam Yakubu ya shaida wa BBC cewa, a gaskiya sakamakon bullar coronavirus a kasar ya sa jama’a da dama da suka saba zuwa cin kasuwa ba su je ba.

Ya ce ” Kasashen da ke makwabtaka da Najeriya wadanda jama’arsu ke zuwa cin kasuwar, yanzu haka duk sun dauke kafafunsu sun bar shigowa kasar”.

Malam Yakubu ya ci gaba da cewa ” Rashin zuwan mutane kasuwar musamman ‘yan wasu kasar ba karamin shafar ciniki ya yi ba”.

Ya ce ” Ada kafin shigowar wannan cuta, ina yin kamar naira 400 zuwa 500 a kowacce rana idan kasuwa ta ci, to amma bayan bullar cutar yanzu sai abin da hali ya yi don da kyar ake cinikin ma”.

Wannan matsala dai ba wai masu shaguna a kasuwar ta shafa ba kadai, hatta mata masu sayar da abinci su ma naji a jikinsu, domin ciniki ya ja sosai.

Laila wata mai sayar da abinci ce a kasuwa ta Suleja d ake ci a duk ranar Lahadi, ta kuma shaida wa BBC cewa, yanayin ciniki sai a hankali domin ba kamar a baya ba.

Ta ce ba mamaki saboda zancen coronavirus da ake ta yi ne ya sa tsoro da fargaba a zukatan mutane shi ya sa jama’a da dama ba su je kasuwar a wannan makon ba.

Bullar coronavirus a Najeriya ta sanya fargaba a zukatan ‘yan kasar lamarin da ya sa gwamnatin kasar ta dauki matakai daban-daban don dakile yaduwarta a tsakanin al’umma.

Ya zuwa yanzu dai a hukumance an samu mutum 30 da suka kamu da cutar a Najeriyar, inda biyu daga cikinsu sun warke har an sallamesu.

More News

Magoya bayan APC da dama sun koma NNPP a Kano

Jam'iyar NNPP ta karɓi magoya bayan jam'iyar APC da dama a jihar Kano. Mataimakin gwamnan jihar Kano, Aminu Abdul Salam Gwarzo shi ne ya karɓi...

APC ta dakatar da Ganduje a matakin gunduma

Mambobin jam'iyyar APC a mazabar da ke Karamar Hukumar Dawakin Tofa a Jihar Kano sun dakatar da Shugaban Jam’iyyar APC na kasa Abdullahi Ganduje. ...

Yadda rikici a kan gishirin N20 ya yi sanadiyyar mutuwar wani mutum a Kano

Wani magidanci mai suna Zakari Hamza mai shekaru 45, ya gamu da ajalinsa a hannun kanen matarsa, wani Magaji Salisu saboda gishirin N20. Dan marigayin,...

Sojoji Sun Kashe Mayaƙan IPOB 5

Dakarun rundunar sojan Najeriya da kuma ta rundunar sojan ruwan Najeriya a ranar Talata sun kashe mayaƙan ƙungiyar IPOB guda biyar a yayin musayar...