
Hakkin mallakar hoto
NurPhoto
Babban jami’i a Kwamiti na Musamman da gwamnatin Tarayyar ta kafa kan cutar korona a Najeriya, Dr Aliyu Sani ya ce babban dalilin da ya sa asibitin Malam Aminu Kano ya rufe dakin gwajin cutar korona shi ne su kansu masu gwajin sun kamu da cutar.
Sai dai Dr Sani bai fadi yawan adadin yawan mutanen da suka kamu da cutar ba.
Dangane da kokawar da ma’aikatan cibiyar gwajin ta Kano suka yi cewa rashin kayan aiki ne ya sa aka dakatar da yin gwajin, Dr Aliyu Sani ya ce “ko a jiya Laraba mun tura kayan gwaji zuwa Kano”, amma ba za su iya amfani da wurin ba saboda bukatar tsaftace wurin.
Wannan batu ba zai rasa nasaba da yadda ba a samu ko da mutum daya ba mai dauke da cutar korona a Kano ranar Laraba ba.
A alkaluman da hukumar da ke dakile yaduwar cutuka ta kasar, NCDC ta fitar da daren Larabar babu masu cutar daga jihar Kano.
Kididdiga ta ranar Talata dai ta nuna jihar na da masu dauke da cutar 73.
Wannan dai na zuwa kasa da mako guda bayan da kimanin mutum uku da suka hada da shugaban kwamiti na musamman kan korona da gwamnatin jihar Kano ta kafa suka kamu da cutar korona.
Dr Aliyu Sani ya ce muna sane da irin halin da jihar Kano take ciki kasancewar idan cutar ta ci gaba da bazuwa a Kano to tamkar gabadaya arewacin Najeriya ya kamu ne.
“Akwai kunshi na musamman da za a bai wa jihar Kano kamar yadda aka bai wa jihar Legas.”
Dangane kuma da yawan mace-macen mutane da aka samu a birnin Kano, Dr Sani ya ce suna ci gaba da bincike domin gano makusudin mace-macen.
Ya ce an kafa kwamitoci daban-daban domin gano cewa ko cutar korona ce ke kisa a Kano ko sankarau ne ko kuma zazzabin Lassa ne.