Coronavirus: Miliyoyin mutane sun rasa damar samun aiki ta shafin LinkedIn

Linkedin

Miliyoyin mutane a sassan duniya sun rasa ayyukansu saboda barkewar annobar korona.

Wata sabuwar kididdiga da manhajar LinkedIn mai samar da ayyukanyi ta Amurka ta fitar ta nuna cewa yawancin tattalin arzikin kasashen duniya na kokarin farfadowa daga durkushewar da ya shiga bayan bullar cutar korona ga kuma matsalar rasa ayyukan yi ta annobar ta haifar.

A yanzu haka kasashen da dama a duniya na kokarin farfado da tattalin arzikinsu da kuma mayar da mutane kan ayyukansu da suka rasa bayan bullar annobar koorna.

Kididdigar ta manhajar Linkedin ta fitar bayan tattara bayanai daga kasashe 15 ya nuna cewa kasashen ba zasu iya ciki gibin ayyukan da suka rasa ba.

Kididdigar ta kuma nuna cewa kasashen turai da Amurka sun gaza cike gibin ayyukan da suka rasa da kaso 50 cikin 100 idan aka kwatanta da bara kamar a yanzu,

Kasashen nahiyar Asiya su da dan dama-dama a cewar kididdigar manhajar ta Linkedin saboda sassauta dokokin kullen da suka yi ya sa al’amuran kasuwanci a kasashen sun dan inganta.

To amma kididdiga daga Sweden da Brazil ta nuna cewa duk da biris din da aka yi da dokar kulle a kasashen hakan bai cimma ruwa ba.

To sai dai kuma kididdigar ta nuna cewa ana samun ci gaba ta fuskar daukar ma’aikata ko samar da aikin yi ga jama’a a wasu yankuna na China da Faransa da kuma Canada.

Kazalika fargabar da ake da ita ta sake barkewar cutar korona a karo na biyu ya tsayar da daukar sabbin ayyuka a wasu kasashe da daman a duniya.

More from this stream

Recomended