Coronavirus: Ma’aikata sun koma bakin aiki a China

Coronavirus

Hakkin mallakar hoto
Reuters

Miliyoyin mutane a China sun fara komawa bakin aiki bayan hutun sabuwar shekarar gargajiya- wanda aka tsawaita don takaita yaduwar coronavirus.

Har yanzu akwai matakan kariya, ciki har rage lokacin da ake yi a ofisoshi don takaita yawan mutane a wuri guda.

An fi mayar da hankali dai a kamfanonin samar da abinci da makamashi da magunguna.

A cibiyar kasuwanci ta Shanghai, ana gwada zafin jikin ma’aikata a tashar jiragen kasa kuma ana ba su shawarwari kan yadda za su kare kansu.

Kawo yanzu, China ta ce yawan mutanen da suka mutu sanadiyyar cutar sun haura dari tara.

A lardin Hubei, inda cutar ta fara barkewa, yawan mutanen da ke kamuwa da ita na ci gaba da karuwa.

Wata tawagar kwararru da HUkumar Lafiya ta Duniya ke jagoranta za ta isa China a yau Litinin don taimakawa a wani bincike kan annobar.

More from this stream

Recomended