
Asalin hoton, Getty Images
Kasashe a fadin Turai na tsaurara matakan kullen korona, sakamakon karuwar wadanda ke kamuwa da cutar cikin hanzari da ake samu a nahiyar.
Wani sabon tsari mai matakai uku ya fara aiki a Ingila, wanda ya raba kasar zuwa matakai uku, wuraren ake da barazanar yaduwar cutar, da wadanda ke da matsakaiciyar barazana da kuma wadanda ke da barazana sosai.
Masu bawa gwamnatin kasar shawara kan harkokin kimiyya sun ce tsarin ya yi sassauci sosai.
Netherlands ta sanar da kulle wani bangaren ta har nan da makwanni hudu masu zuwa, kana ta tilastawa jama’a yin amfani da takunkumi.
A jamhuriyyar Czech ma tuni aka soma sake rufe makarantu, wuraren shan barasa da kuma dandali har nan da makonni uku.
Ministan lafiyar kasar Roman Pry-mula, ya ce mutane da dama sun saki jiki sakamakon sassauta dokokin kulle a baya.
Kasashen Turai masu yawa sun bude iyakokinsu da makwabtansu na Tarayyar Turai bayan shafe watanni da aka kullesu kuma aka hana tafiye-tafiye saboda rage yaduwar annobar.
Hukumar gudanarwa ta Tarayyar Turai ce ta bukaci dukkan kasashen da ke cikin tarayyar da su kawo karshen matakan gaggawa da suka dauka, domin ta ce matakan ba su da tasirin da ake bukata saboda matakan bayar da tazara da kasashen suka fitar na cimma bukatun da ake da su na dakatar da bazuwar annobar.
Sai dai ana ganin janye matakan ya taimaka matuka gaya wajen sake samun yaduwar cutar a yanzu.
A wasu kasashen dai cutar na a kan matakin zagaye na uku a yanzu haka.