Coronavirus: ‘Gwamnatin tarayya ta yi watsi da Kano’

Gwamna Abdullahi Ganduje

Hakkin mallakar hoto
KANO STATE

Image caption

Gwamna Abdullahi Ganduje

A daidai lokacin da Najeriya ke kokarin shao kan annobar korona, jihar Kano da ke arewacin kasar ta sami kanta cikin wani mawuyacin hali.

Al’ummar jihar suna jimamin mace-macen masu daure kai da ke faruwa musamman a cikin birnin Kano.

Gwamnatin jihar ta dauki matakan killace al’ummar jihar a gida, bayan kulle dukkan iyakokin jihar da labarin bazuwar cutar korona ya rika karuwa.

Bayanan da ke fitowa daga Kanon dai na nuna da cewa lamarin ya riga ya gagari Kundila, domin wasu na ganin tamkar gwamnatin jihar ta rasa alkibla kuma lissafi ya kwace mata.

Suna kuma ganin gazawarta ta fito fili a yaki da cutar korona duk kuwa da ikirarin da ta jima tana yi na cewa ta shirya tun ma gabanin bullar cutar a jihar.

Farfesa Sadiq Isa Abubakar shugaban cibiyar yaki da cuttuka masu yaduwa na asibitin Malam Aminu Kano da jami’ar Bayero, dan kwamitin yaki da cutar korona a jihar ne.

“Halin da ake ciki hali na abin tsoro, bayan kwanaki da aka shafe ana yin gwaje-gwajen masu dauke da cutar korona, yanzu sai aka sami tsaiko.”

Ya kara da cewa: “Jinkirin da ake samu kafin a fitar da sakamakon yana tsoratar da mu ma’aikatan lafiya”.

Babban abinda ya fi daga hanakalin jama’a a yanayin da ake ciki na rashin sanin hakikanin illar da korona ke yi a jihar, da ma haske kan kiyasin mutanen dake dauke da cutar shi ne yawan mace-macen da ake samu a binin fiye da kowane lokaci a baya.

A cikin mako guda fitattun mutane da masu shekaru na kwanta dama a kusan dukkanin unguwannin jihar.

Cikin wadanda aka rasa daga Asabar zuwa Lahadi akwai farfesoshi guda hudu wanda na baya-bayannan shi ne Farfesa Balarabe Maikaba, na tsangayar nazarin aikin jarida a jami’ar Bayero dake Kano.

Abinda ke nan ya sa wasu masana harkar lafiya a wajen Kano ke nuna damuwa kan munin lamarin, kuma suke cewa da alama cutar korona ce ke wannan kisan mummuken.

Farfesa Usman Yusuf kwararren likita ne kuma tsohon shugaban inshorar lafiya na Najeirya.

“Duk inda ka ji wani dattijo ya mutu a ko ina a duniya – daga New York har Wuhan har Ghana – ko wace cuta ya ke da ita, yawanci za ka taras Covid-19 ce dalilin mutuwarsa.”

Ya ce, “Irin wadannan dattijan da dama suna fama da wasu matsalolin rashin lafiya, kamar ciwon sikari, hawan jini da cutar huhu, irinsu ta ke zuwa ta daka ta tafi mana da su”.

Yanayin da ake ciki dai a Kanon ya sa uwar jam’iyyar PDP ta kasa ta fitar da sanarwa tana mai cewa abinda ke faruwa a Kano abin takaici ne yadda gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta kasa daukar matakai na zahiri kan wannan batun mai tayar da hankali.

Daya daga jagororin PDP din a Kano Umar Haruna Dogowa ya ce a zahiri take cewa gwamnatin jihar ta gaza.

“Sauran jihohi kamar Legas da Ogun sun taka rawar gani kan yaki da wannan cutar, amma a jihar Kano babu wani abin a zo a gani da aka yi. Me yasa ba a samar da irin cibiyoyin bincike kamar yadda aka samar a wasu jihohin ba?”

Daya daya manyan abubuwan da suka fi daukar hankalin kan batun na Kano shi ne dakatar da gwajin cutar korona a cibiya daya tilo a Kano tsawon kwanaki.

To sai dai a yanzu a iya cewa matsalar ta kusa zuwa karshe, kamar yadda Dr. Isa Abubakar Aliyu daya daga cikin wadanda suke gwajin cutar ta korona a Kano ke cewa.

“Dama an kulle cibiyar ne domin a yi feshin magani. Feshin na daukar awa 48 kuma mun yi nasarar feshe ko ina.”

Ya ce ranar Litinin za a ci gaba da ayyukan gwaje-gwaje a cibiyar.

Masu lura da al’amura dai na cewa ya kamata Kano ta yi koyi da jihar Lagos da ta kafa cibiyoyin daukar samfurin gwaji a kowace karamar hukumar jihar, yayin da kuma ake da wuraren gwaji har uku, ta yadda za a samu hakikanin bayanin abinda ke faruwa a jihar ta Kano.

More News

Tayoyin jirgin saman Max Air sun fashe a Yola

Jirgin saman kamfanin Max Air ƙirar Boeing 737 mai rijistar namba 5N-ADB dake ɗauke da fasinjoji 118 da ma'aikata 6 ya gamu da matsala...

ÆŠan majalisar wakilai ta tarayya ya mutu

Hon. Olaide Akinremi Jagaba mamba a majalisar wakilai ta Najeriya dake wakiltar mazaɓar Ibadan North a majalisar ya mutu. Kawo yanzu babu cikakken bayani kan...

Gwamnan Kano ya sanya hannu kan dokar yin gwajin lafiya kafin aure

Gwamnan jihar Kano, Engr Abba Kabir Yusuf ya sanya hannu kan wata doka za ta tilastawa masu yin aure yin wasu gwaje-gwajen lafiya gabanin...

An kashe kwamandan soji a Katsina

An kashe kwamandan sojoji na wani sansanin soji da ke Sabon Garin Dan’Ali a karamar hukumar Danmusa a jihar Katsina a wani harin kwantan...