
Hakkin mallakar hoto
Getty Images
Yawan mata masu zuwa awo ko renon ciki ya ragu daga miliyan 1.3 zuwa dubu 655
Ministan Lafiya na Najeriya ya ce kimanain kashi 50 cikin 100 na marasa lafiya masu zuwa asibitoci a duba su sun daina zuwa asibitocin.
Dr Osagie Ehanire ya ce adadin mata masu juna biyu da ke zuwa asibiti da kuma ayyukan riga-kafi sun ragu matuƙa, tun daga lokacin da aka samu bullar cutar korona a kasar.
Dr Ehanire wanda ya yi bayani a wurin taron manema labarai na kullum da kwmaitin yaƙi da cutar korona na ƙasa ke yi a Abuja, ya ce adadin marasa lafiya da ke zuwa asibitoci a matakin je-ka-ka-dawo, wato wadanda ba a kwantar da su ba, ya ragu daga mutum miliyan hudu zuwa miliyan biyu a duk rana.
Haka nan yawan mata masu zuwa awo ko renon ciki ya ragu daga miliyan 1.3 zuwa dubu 655, yayin da ayyukan riga-kafi suka yi ƙasa ta kusan rabi.
Adadin karɓar haihuwa da ƙwararrun ma’aikatan kiwon lafiya ke yi, ya ragu sosai.
Amma Ministan bai yi ƙarin haske kan dalilan da suka haifar da wannan gagarumar raguwar ba, ya yi nuni da cewa matakan takaita zirga-zirga da aka ɗauka don yaƙi da cutar korona ka iya kasancewa cikin dalilan.
Sai dai kuma rahotanni daga sassa daban-daban na Najeriya na nuna cewa marasa lafiya da dama sun daina zuwa asibiti saboda tsoron kamuwa da cutar korona, wasu kuma likitocinsu ke ba su shawarwarin kiwon lafiya ta waya domin rage yawan mutane a asibiti.
Har wa yau, bayanai na nuna cewa an rufe asibitoci da dama musamman masu zaman kansu, yayin da a wasu wuraren kuma ake ɗari-ɗari da karɓar marasa lafiya, a lokacin da su kuma hukumomi hankalinsu ya fi karkata ga cutar Korona.
Shugaban Ƙungiyar Likitoci ta Najeriya, Dr Francis Faduyile, ya shaida wa BBC cewa samun raguwar adadin marasa lafiya da ke zuwa asibotoci, da mata masu juna biyu, da kuma ayyukan riga-kafin da kusan kashi 50 cikn 100, ka iya ƙara jefa mata da ƙananan yara da kuma dattijai cikin haɗari.
Amma Ministan Lafiya Dr Ehanire ya ce gwamnati na ɗaukar matakan tabbatar da an koma ga ayyukan kiwon lafiya na yau da kullum kamar yadda aka saba.