Coronavirus: Chana ta amsa gazawa

Za a fara tilastawa jama'a rufe baki da hanci da nufin rage bazuwar cutar Coronavirus

Za a fara tilastawa jama’a rufe baki da hanci da nufin rage bazuwar cutar Coronavirus

A karon farko gwamnatin Chana ta amsa cewa anyi sanyi jiki wurin tunkarar cutar Coronavirus.

Hakama ta bayyana cewa an samu kalubale da ya kawo tsaiko wurin tunkarar cutar.

Kwamitin da gwamnatin ta kafa ya ce babu makawa dole ne hukumar agajin gaggawa ta shawo kan yaduwar wannan cuta ta Coronavirus.

Kuma tuni an fara ganin sauyi, inda aka shiga kargame duk wata kasuwa da ake sayar da dabbobi da ake zargin daga can ne wannan cuta mai hana numfashi ta bulla.

Kawo yanzu mutane 20,000 sun kamu yayin da 425 su ka mutu.

Bincike ya nuna cewa mutun 3,000 ne ke kamuwa da Coronavirus a duk rana.

Kuma tuni adadin wadanda suka mutu ya zarta na cutar Sars wadda akayi a shekarar 2003.

An samu kamuwar mutun 150 a wajen Chana tare da mutuwar mutun daya a Philippines.
Rahotanni sun kuma nuna cewa ko a wajen Chana wadanda suka kamu da cutar sun kai mutun 150 tare da rahoton mutuwa daya a Philippines.

Coronavirus na farawa ne da zazzabi daga nan kuma sai tari wanda daga karshe zai kai me fama da ita kwance.

Wannan annoba ta yi sanadiyyar mummunar faduwar hannayen jarin Chana a ranar litinin, wanda ba ta taba gani ba a cikin shekara hudu.

Gwamnatin Chana hakama ta zargi Amurka da tsoratar da al’umma da kuma kai lamarin inda bai kai ba.

Yanzu dai hukumomi sun soma tilastawa yankunan da ke da yawan jama’a miliyan 300 saka kyallen rufe baki da hanci, yayin da ake ta fadi tashin neman maganin cutar Coronavirus.

More from this stream

Recomended