
Hakkin mallakar hoto
Kwankwaso
Tsohon gwamnan jihar Kano Injinya Rabi’u Musa Kwankwaso ya yi karin bayani kan abin da ya sa ya bayar da gudunmuwar asibiti ga gwamnatin abokin hamayyarsa Abdullahi Umar Ganduje don jinyar masu fama da cutar korona.
Kwankwaso ya ce “wannan gini an tanade shi ne domin amfanin mambobinmu na Kwankwasiyya da ma dukkan dan jihar Kano.
“Kuma bayan kammala shi mun shigo da kayan aiki sai ga wannan ciwo ya shigo. Shi ya sa muka sayo kayyakin yaki da korona.
”Akwai ma wasu karin wurare kamar dakunanmu na taro da idan bukatar bayar da su ta taso to za mu bayar da su. Amma muna fata Allah ya takaita.”
Tsohon gwamnan ya kuma yi karin haske kan mahawarar da ake yi dangane da gadajen karfe da aka tanada a asibitin, maimakon irin gadajen da ake amfani da su a asibitoci.
“Kayan da muka yi oda ba su iso ba. Wadannan gadajen da ma suna cikin wurin.”
Kwankwaso ya ce ya bayar da asibitin ne har zuwa lokacin da aka ga bayan cutar korona.
Sai dai ya ce har yanzu kwamitin da ke yaki da cutar ta korona bai tabbatar da karbar asibitin ba ko akasin haka.
Zuwa yanzu masu cutar korona sun kai 73 a jihar Kano inda tuni kuma ta yi ajalin mutm daya.