Cire Tallafin Mai: Gwamnatin Tarayya Ta Shirya Biyan N5000 Ga Iyalai Miliyan 10

Gwamnatin tarayya za ta biya N5000 ga iyalai miliyan 10 a matsayin tallafin rage raɗaɗin cire tallafin man fetur da ake shirin yi.

Kamar yadda rahoton jaridar Daily Trust ya nuna a kowane wata gwamnatin tarayya za ta kashe biliyan N50 a kowane wata cikin kuɗin da Babban Bankin Duniya ya bayar da bashi domin aiwatar da shirin.

Ministan kasafin kudi da tsare-tsare, Hajiya Zainab Shamsuna Ahmad ce ta bayyana haka ranar Lahadi a wurin taron Babban Bankin Duniya da Asusun Lamini na IMF dake gudana a birnin Washington DC.

Zainab ta ce tuni aka gama duk wata tattaunawa kan batun kuɗin yanzu kawai amincewar majalisar ƙasa ake bukata domin a fara aiwatar wa.

More from this stream

Recomended