Cire Tallafin Mai: Gwamnatin Tarayya Ta Cigaba Da Tattaunawa Da Kungiyoyin Kwadago

Gwamnatin tarayya ta cigaba da tattaunawa da kungiyoyin kwadago na NLC da TUC kan matakan za a bi domin rage raɗaɗin cire tallafin man fetur.

A ranar 5 Yuni ne kungiyoyin kwadago suka janye shiga yajin aikin da suka shirya yi domin nuna adawar su ga cire tallafin bayan da suka gudanar da taro da wakilan gwamnati.

Taron na ranar Litinin ya gudana ne a ɗakin taro na ofishin shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Femi Gbajabiamila dake Aso Rock.

Shugaban kungiyar NLC Joe Ajaero na TUC Festus Osifo da sauran shugabannin kwadago na daga cikin mahalarta taron.

More from this stream

Recomended