China za ta taimaki Najeriya a yaki da yan ta’adda

Yu Dunhai jakadan kasar China a Najeriya  ya ce China za ta cigaba da taimakawa Najeriya a yakin da take da ta’addanci.

Dunhai ya bayyana haka ne a cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na X da aka fi sani da Twitter a baya a ranar Alhamis bayan da ya yi wata ganawa da mai bawa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Mallam Nuhu Ribadu.

Ya ce kasar China na kalubalantar kowane irin tsoma bak na wata  kan matsaolin cikin gida na Najeriya ” ta hanyar fakewa da addini da kuma yancin dan adam”

Da yake magana a wani taron manema a ranar Talata a birnin, Beijing mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen China ya yi kashedi  kan katsalandan  a cikin harkokin cikin gida na Najeriya.

Ning ya fadi haka ne lokacin da yake amsa tambaya kan barazanar da shugaban kasar, Amurka Donald Trump ya yi na daukar matakin soja akan Najeriya kan zargin da yayi na musguna wa Kiristoci tare da yi musu kisan kare dangi.

More from this stream

Recomended