Godwin Emefiele, gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), ya ce bankuna za su ci gaba da karbar tsoffin takardun kudi na Naira bayan wa’adin da aka kayya
Emefiele ya yi magana ne a yanzu yau ranar Talata lokacin da ya bayyana a wani zama na tattaunawa da kwamitin rikon kwarya na majalisar wakilai kan batun sake fasalin kudin da kuma canza canjin naira.
Ya ce CBN kuma za ta karbi tsohuwar Naira daga bankuna bayan wa’adin ranar 10 ga watan Fabrairu.
Emefiele ya yi tsokaci kan dokar CBN ta umurci babban bankin ya ci gaba da karbar tsofaffin takardun kudi bayan karewar wa’adin..