CBN Ya Bayyana Dalilin Da Ya Sa Ake Samun Karancin Takardun Kuɗin Naira

Babban Bankin Najeriya CBN ya bayyana dalilin da ya sa ake samun karancin takardun kuɗin naira a faɗin kasa baki ɗaya.

Hakan na zuwa ne biyo bayan jerin korafe-korafe da masu amfani da bankuna ke yi na fuskantar karancin takardun naira a na’urar ATM, cikin bankuna wajen masu POS dama masu sauya kuɗaɗen kasashen waje.

A wata sanarwa da sashen hulda da ƴan jarida na CBN ya fitar babban bankin ya ce yadda bankunan kasuwanci ke kwasar takardu kudi da yawa daga rassan CBN daban-daban na daga cikin dalilin da ya haifar da ƙarancin kudin.

Har ila yau sanarwar ta kara da cewa yadda kwastomimin banki suke yawan cire kudi saboda fargabar dawo da dokar takaita amfani da zallar kudi shi ma ya taimaka wajen samun karancin takardar kudin na naira.

CBN ya ce akwai isassun takardun kuɗin naira da suke zagayawa a hada-hadar kasuwanci da ake a Najeriya.

More News

Mutum ɗaya ya mutu wasu sun jikkata a hatsarin motar tankar gas

Mutum ɗaya ya mutu a yayin da wasu biyu suka jikkata bayan da wata tankar gas tayi bindiga ta kama da wuta a Ita-Oshin...

Ɗan Boko Haram Ya Miƙa Kansa Ga Sojoji

Wani mamba a ƙungiyar ƴan ta'adda ta Boko Haram ma suna, Sajeh Yaga ya miƙa kansa ga dakarun rundunar Operation Haɗin Kai dake arewa...

EFCC ta kama wasu masu hada-hadar canjin kuɗaɗe

Hukumar EFCC dake yaƙi da masu yiwa tattalin arzikin ƙasa ta'annati ta kama wasu mutane 34 da take zargi suna da hannu wajen yiwa...

Mutane uku sun mutu a ruftawar wani ginin bene a Kano

Hukumar Bada Agajin Gaggawa Ta Ƙasa NEMA ta tabbatar da mutuwar mutane uku bayan da wani bene mai hawa uku ya ruguzo a unguwar...