Burnley ta taka wa Liverpool burkin cin wasa a gida

Andy Robertson scores for Liverpool against Burnley

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Kwallon da Robertson ya ci a Anfield shi ne na 150 da Liverpool ta zura a raga a wasa 58 ba a doke ta ba a gida

Burnley ta taka wa Liverpool burki na kokarin cin dukkan wasanni gida a kakar tamuala, bayan da ta buga 1-1 a gasar Premier League ranar Asabar a Anfield.

Robertson ne ya fara ci wa Liverpool kwallo a minti na 34, yayain da Burnley ta farke bayan da suka koma karawar zagaye na biyu ta hannun Rodriguez.

Hakan na nufin Liverpool wacce ta lashe kofin Premier na bana, ba za ta kafa tarihin lashe dukkan wasanni a gida ba a bana.

Tana bukatar doke Chelsea a wasan karshe a kakar bana ta zama ta yi nasara a fafatawa 18 a Anfield a shekarar nan.

Saura wasanni uku a karkare kakar shekarar nan, Liverpool tana da damar kafa tarihin hada maki fiye da 100, domin haura wanda Manchester City ta yi a kakar 2017-18.

Kawo yanzu Burnley ta yi wasa biyar ba a doke ta ba, tun bayan da aka ci gaba da wasannin Premier League, wanda cutar korona ta sa aka dakatar a cikin watan Maris.

Rabon da Burnley ta yi rashin nasara a gasar bana tun 5-0 da Manchester City ta dura mata wata uku da suka wuce.

Wannan canjaras da ta yi ya sa Burnley tana ta tara a kan teburi tana kuma sa ran samun gurbin shiga gasar Zakarun Turai ta Europa League ta badi.

Tuni dai burin Liverpool ya cika na lashe kofin Premier League na bana kuma na farko tun bayan shekara 30 kuma na 19 jumulla.

Liverpool na harin kungiyar da ta fi lashe wasanni a bana, kawo yanzu ta ci karawa 32 kuma ta gaba a samun maki mai yawa a gida 55.

More from this stream

Recomended