
A ranar Talata aka shirya shugaban ƙasa, Muhammad Buhari zai tafi kasar Saudiyya domin ziyarar aiki.
A wata sanarwa da aka fitar ranar Litinin mai dauke da sahannun mai magana da yawun shugaban ƙasa , Mallam Garba Shehu ta ce ziyarar da za ta ɗauki tsawon kwanaki 8 ita ce ziyarar Buhari ta karshe zuwa Saudiyya a matsayin shugaban kasa.
Shehu ya ce yayin da yake Saudiyya Buhari zai yi aikin Umarah.
Buhari zai samu rakiyar wasu daga cikin masu taimaka masa.