Buhari Ya Zabi Justice Ishaq Ya Wakilci Nigeria A ICC

Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya zabi shugaban alkalin alkalai na birnin Abuja, Alkali Ishaq Usman a matsayin wanda zai wakilce Najeriya domin zama babban lauya a kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa (ICC).

Kotun wacce ta fara aiki ranar 1 ga watan Yulin shekarar 2002 a matsayin kotun kasa da kasa wacce ke birnin Hague na kasar Netherlands.

ICC na da ikon hukunta mutane da ake tuhuma da aikata laifukan yaki, da keta hakkin bil adama da cin zarafi da dai sauransu.

A ranar 7 zuwa 17 ga watan Disambar wannan shekarar ne ake sa ran gudanar da zaben mukamin.

Za a gudanar da zaben a hedikwatar majalisar dinkin duniya da ke birnin New York kuma za a zabi alkalai 6 wadanda zasu cika kashi daya na 3 na kotun.

Kafin yanzu, Hon. Ishaq Usman Bello ya yi aiki a kwamitoci da suka shaki shari’a daban daban.

Ya kuma yi muhimman ayyuka kamar wakiltar Najeriya a kotu da jagorantar zaman da suka shafi shari’ar zabe.

More News

Zanga-zanga: An jibge Æ´an sanda 4200 a Abuja

Rundunar Æ´an sandan birnin tarayya Abuja ta tura Æ´an sanda 4200 gabanin zanga-zangar da za a gudanar a cikin watan Agusta. Kamar yadda masu shirya...

Kamfanin NNPC ya shirya daukar karin ma’aikata

Kamfanin mai na Nigerian National Petroleum Company Limited ya shirya daukar karin ma’aikata.Kakakin kamfanin na NNPC, Olufemi Soneye, ya tabbatar da hakan a wata...

Ya kamata matasa su yi haÆ™uri zanga-zanga ba ita ce mafita ba – Sarkin Zazzau

Sarkin Zazzau, Mai Martaba Ahmed Nuhu Bamalli ya ce matasa su ƙara haƙuri da gwamnatin tarayya su janye zanga-zangar da suka shirya gudanarwa a...

Zanga-zanga: Tinubu ya gana da gwamnonin APC

Shugaban ƙasa, Bola Ahmad Tinubu ya gana da gwamnonin da aka zaɓa ƙarƙashin jam'iyar APC. Taron ganawar da aka gudanar a fadar shugaban ƙasa ta...