
Gwamnatin tarayya karkashin jagorancin ma’aikatar agaji da jinkai da kuma cigaban al’umma, ta tura tireloli 110 dankare da kayayyakin abinci zuwa jihar Kano domin rabawa mabukata da marasa galihu a fadin jihar.
Bashir Ahmad mataimaki na musamman ga shugaban kasa ne ya bayyana hakan a shafin sa na facebook cikin wannan daren. Inda ya ce yanzu haka kayan tallafin suna kan hanyar zuwa Kano.