Buhari ya saka dokar hana fita ta mako biyu a Kano – AREWA News

Shugaban kasa Muhammad Buhari ya ayyana saka dokar zaman gida ta mako biyu a fadin Kano baki daya.

Buhari ya bayyana haka ne cikin jawabin da ya yi wa yan Najeriya ranar Litinin.

Shugaban kasar ya ce dokar hana fitar da ya saka a Kano ta mako biyu zata fara aiki ne nan take daga yau.

Ya ce a yayin da dokar take aiki gwamnatin tarayya za ta mayar da hankali kacokan kan jihar ta hanyar aikewa da jami’an kiwon lafiya dama kayan aiki domin ganin an shawo kan matsalar mace-macen dake faruwa a birnin.

An dai ta yin kiraye-kiraye kan gwamnatin tarayya ta kawowa jihar dauki kan halin da take ciki.

More from this stream

Recomended