
Babban dan kasuwa, Alhaji Dahiru Barau Mangal na cigaba da karbar manyan mutane dake kai masa ziyarar ta’aziyyar matarsa.
A ranar Laraba tsohon shugaban kasa, Muhammad Buhari ya shiga sahun wadanda suka kai wa dan kasuwar ziyarar ta’aziyyar matarsa, Hajiya Aisha Dahiru Mangal.
Gwamna Dikko Umaru Radda shi ne ya raka Buhari gida Mangal.
Tsohon mai taimakawa shugaban kasar, Sabiu Tunde na tare da Buhari a yayin ziyarar.
Buhari ya yi addu’ar Allah Ya jikan marigayiyar Ya kuma bawa iyalanta hakurin jure rashin da suka yi.