Buhari ne ya lalata Najeriya, in ji Rarara

Shahararren mawakin siyasar Hausa, Dauda Kahutu, wanda aka fi sani da Rarara, ya zargi tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari da mikawa shugaban kasa Bola Tinubu ƙasa a cikin mummunan yanayin tattalin arziki.

Rarara, wanda ya fito fili bayan ya fitar da wakoki da dama ga Buhari, ya kuma ce ya yi nadamar goyon bayan tsohon shugaban.

Ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Kano ranar Alhamis.

Ya yi mamakin dalilin da ya sa har yanzu gwamnatin Tinubu ba ta bayyana ra’ayinsu game da sakaci da gwamnatin Buhari ta yi ba.

Mawakin ya kuma yi ikirarin cewa an hana shi damar ganawa da shugaban kasa Bola Tinubu domin ba shi shawara kan yadda zai fallasa almundahana da gwamnatin da ta shude ta yi.

More News

Gwamantin Kano na kashe naira biliyan 1.2 duk wata don samar da ruwan sha—Kwamishina

Gwamnatin jihar Kano na kashe kimanin naira biliyan 1.2 duk wata don samar da ruwan sha na tafi da gidanka a cikin babban birnin...

Wasu É—aliban Jami’ar Jihar Nasarawa sun mutu a lokacin turmutsutsin karÉ“ar tallafin abinci

Dalibai biyu daga Jami’ar Jihar Nasarawa da ke Keffi (NSUK) sun rasa rayukansu a wani turmutsitsi da ya barke a lokacin da suke kokarin...

Jarumin Nollywwood, Mr. Ibu, ya rasu

Jarumin Nollywood, John Okafor, wanda aka fi sani da "Mr Ibu", ya rasu yana da shekaru 62. Emeka Rollas, shugaban kungiyar Actors Guild of Nigeria,...

Miyetti Allah ta nemi a cafke Sunday Igboho saboda barazanar yaƙar Fulani

Kungiyar Miyetti Allah Cattle Breeders Association of Nigeria, MACBAN, ta yi kira da a damke wani dan kabilar Yarbawa, Sunday Adeyemo, wanda aka fi...