Brexit: ‘Yan majalisar Birtaniya sun karbe iko daga hannun Boris Johnson

Boris Johnson speaking outside Downing Street

Hakkin mallakar hoto
PA Media

Image caption

Firai minista Boris Johnson na jawabi a gaban fadar gwamnatin Birtaniya

‘Yan jam’iyyar Conservative mai mulkin Birtaniya da na bangaren adawa sun kayar da gwamnatin kasar a mataki na farko na kokarin da suke yi na hana Birtaniya ficewa daga Tarayyar Turai ba tare da yarjejeniya ba.

Majalisar ta gudanar da zabe inda masu goyon bayan ta karbe ikon gudanarwa suka kayar da masu goyon bayan Firai ministan da kuri’u 328, inda ya sami 301.

Wannan na nufin za su iya gabatar da kudurin doka da zai jinkirta ranar ficewar Birtaniya daga Tarayyar ta Turai.

Amma Firai ministan ya fusata da matakin da ‘yan majalisar suka dauka, kuma ya yi alkawarin gudanar da wani kudurin a yi zaben gama gari.

Image caption

Jagoran jam’iyyar adawa ta Labour Jeremy Corbyn

Jagoran jam’iyyar adawa ta Labour Jeremy Corbyn ya nemi majalisar da ta tabbata an gabatar da kudurin hana Birtaniya ficewa daga Tarayyar Turai kafin a gudanar da zaben.

Duka-duka, ‘yan majalisa 21 ne daga jam’iyyar ta Conservative – ciki har da wasu tsofaffin ministoci – suka hada kai da ‘yan adawa domin kayar da gwamnatin a kan wannan muhimmin batu.

Bayan da aka kammala zaman majalisar, fadar Firai minista da ke lamba 10 Downing Street ta fitar da wata sanarwa da ke cewa za a nemi korar ‘yan majalisar da suka yi boren daga jam’iyyar.

Firai ministan ya so ya tsorata ‘yan majalisar ne da gargadin da ya yi na korarsu daga jam’iyyar, amma hakan bai samu ba.

More News

Yawan Mutanen Da Suka Mutu A Wutar Da Wani Matashi Ya Cinnawa Wani Masallaci A Kano Sun  Karu Zuwa 16

Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta ce yawan mutanen da suka mutu sakamakon wutar da wani ya cinnawa wani masallaci a ƙauyen Gadan a...

An fara rushe wasu gine-gine 500 a kasuwar Karmo dake Abuja

Hukumar FCTA dake kula da birnin tarayya Abuja ta fara rushe gine-gine sama da 500 da aka yi ba bisa ka'ida ba a kasuwar...

Tinubu ya tarbi shugaban kasar Senegal Bassirou Faye a fadar Aso Rock Villa

A ranar Alhamis ne shugaba Bola Tinubu ya tarbi shugaban kasar Senegal Bassirou Faye a fadar Aso Rock Villa, a ziyarar da Faye ya...

NEMA ta karɓi ƴan Najeriya 150 da aka dawo dasu gida daga ƙasar Chad

Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Ƙasa NEMA ta ce ta karɓi ƴan Najeriya 150 da aka dawo da su bayan da su ka maƙale...