Brexit: An cimma yarjejeniyar ficewar Birtaniya daga EU | BBC news

Stephen Barclay, Boris Johnson, Jean-Claude Juncker and Michel Barnier

Birtaniya da Tarayyar turai sun cimma yarjejeniyar ficewar Burtaniyar daga Tarayyar gabanin wani taron shugabannin turai a Brussels.

Boris Johnson da Jean-Claude Juncker ya bayyana yarjejeniyar da “adalci”, oinda shi kuma shugaban hukumar tarayyar ta turai ya ce babu bukatar tsawaita ficewar Birtaniyar daga EU.

Ya ce ” tun da mun cimma yarjejeniya babu bukatar tsawaita ranar fitar.”

Cimma yarjejeniyar dai za ta kwarara wa firai ministan gwiwa duk da cewa har yanzu yana fuskantar kalubalen gamsar da ‘yan majalisa su yi amanna da yarjejeniyar ranar Lahadi, a dai-dai lokacin da jam’iyyar DUP ta Northern Ireland ke adawa da yarjejeniyar.

  • Shin ko talauci na raguwa a duniya?
  • ‘Mai karfin fada a ji’, wane ne Mamman Daura?

Mista Johnson ya bukaci ‘yan majalisar da su “hada kai” domin ganin an warware batun yarjejeniyar”.

Ya kara da cewa “Yanzu ne lokacinmu na ficewa daga Burtaniya sannan mu yi aiki tare wajen sake gina tubalin alakarmu da EU.”

Mista Johnson ya kuma ce ya kamata Burtaniya ta fice daga Tarayyar Turai “ba tare da bata lokaci ba” ta yadda gwamnati za ta samu damar mayar da hankalinta ga al’amuran cikin gida.

Firai ministan ya sake nanata cewa Birtaniya za ta fice daga EU a ranar 31 ga watan Oktoba.

To sai dai akwai yiwuwar za a aiya tilasta shi ya nemi karin kwanakin ficewar kasar tasa amma kuma shugabannin kasashen na Turai 27 ne ke da damar yin hakan.

To sai dai a wata sanarwa, jam’iyyar Democratic Unionist Party wadda gwamnati ke dogaro da ita wajen taimaka mata, ta yi watsi da yarjejeniyar.

“Wadannan tsare-tsare ba za su amfani tattalin arzikin Northern Ireland ba sannan sun zubar da kimar tarayyar turai.”

Hakkin mallakar hoto
PA Media

Me yarjejeniyar ta kunsa?

Yarjejeniyar na kamanceceniya da wadda Theresa May ta mika a bara, dan banbancin da ke tsakani shi ne daftari kan Northern Ireland.

  • Birtaniya za ta martaba dokokin Tarayyar Turai har zuwa karshen 2020, watakila ma fiye da haka, domin samun damar sauya tsarin kasuwanci.
  • Burtaniya za ta biya tsabar kudin rabuwa har £33bn
  • Za a tabbatar da kare hakkin duk wani dan Tarayyar Turai da ke zaune a Burtaniya da kuma ‘yan Burtaniya da ke zaune a kasashen EU.

Hakkin mallakar hoto
PA Media

More News

Yawan Mutanen Da Suka Mutu A Wutar Da Wani Matashi Ya Cinnawa Wani Masallaci A Kano Sun  Karu Zuwa 16

Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta ce yawan mutanen da suka mutu sakamakon wutar da wani ya cinnawa wani masallaci a ƙauyen Gadan a...

An fara rushe wasu gine-gine 500 a kasuwar Karmo dake Abuja

Hukumar FCTA dake kula da birnin tarayya Abuja ta fara rushe gine-gine sama da 500 da aka yi ba bisa ka'ida ba a kasuwar...

Tinubu ya tarbi shugaban kasar Senegal Bassirou Faye a fadar Aso Rock Villa

A ranar Alhamis ne shugaba Bola Tinubu ya tarbi shugaban kasar Senegal Bassirou Faye a fadar Aso Rock Villa, a ziyarar da Faye ya...

NEMA ta karɓi ƴan Najeriya 150 da aka dawo dasu gida daga ƙasar Chad

Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Ƙasa NEMA ta ce ta karɓi ƴan Najeriya 150 da aka dawo da su bayan da su ka maƙale...