Borussia Dortmund ta dauki Erling Braut Haaland

Haaland

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Kungiyar Borussia Dortmund ta dauki Erling Braut Haaland daga Red Bull Salzburg.

Dormund ta cimma yarjejeniyar fam miliyan 17.1, kudin kunshin kwantiraginsa ta barin Red Bull.

Dan kwallon tawagar Norway, mai shekara 19, ya rattaba hannu da kungiyar ta Jamus har zuwa karshen kakar tamaula ta 2024.

Haaland ya koma Salzburg da taka leda daga kungiyar Molde ta Norway a watan Janairu.

Rahotanni sun ce Manchester United da Juventus sun yi zawarcin dan kwallon.

Haaland ya ci kwallo 16 a wasa 14 da ya buga wa Salzburg a bana, har da guda takwas da ya ci a gasar Champions League.

Salzburg ce ta yi ta uku a rukuni na biyar, wanda Liverpool ta yi ta daya.

More News

Yawan Mutanen Da Suka Mutu A Wutar Da Wani Matashi Ya Cinnawa Wani Masallaci A Kano Sun  Karu Zuwa 16

Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta ce yawan mutanen da suka mutu sakamakon wutar da wani ya cinnawa wani masallaci a ƙauyen Gadan a...

An fara rushe wasu gine-gine 500 a kasuwar Karmo dake Abuja

Hukumar FCTA dake kula da birnin tarayya Abuja ta fara rushe gine-gine sama da 500 da aka yi ba bisa ka'ida ba a kasuwar...

Tinubu ya tarbi shugaban kasar Senegal Bassirou Faye a fadar Aso Rock Villa

A ranar Alhamis ne shugaba Bola Tinubu ya tarbi shugaban kasar Senegal Bassirou Faye a fadar Aso Rock Villa, a ziyarar da Faye ya...

NEMA ta karɓi ƴan Najeriya 150 da aka dawo dasu gida daga ƙasar Chad

Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Ƙasa NEMA ta ce ta karɓi ƴan Najeriya 150 da aka dawo da su bayan da su ka maƙale...