Boko Haram: Shin Buhari zai iya magance matsalar kungiyar kuwa? | BBC Hausa

Buhari

Bayanan hoto,
Buhari ya sha cewa sun kawo karshen Boko Haram

Zargin da gwamnan jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya ya yi cewa jami’an tsaron ƙasar na yin zagon ƙasa a ƙoƙarin murƙushe ƙungiyar Boko Haram ya sake aza babbar alamar tambaya game da ko da gaske Shugaba Muhammadu Buhari yake yi cewa yana son kawar da matsalar mayakan kungiyar kafin ya sauka daga mulki.

Wannan na zuwa ne yayin da jihar Borno ke ganin ƙaruwar hare-haren ‘yan ta-da-ƙayar-baya.

A makon jiya ma sai da Gwamna Babagana Zulum da kansa ya tsallake rijiya da baya lokacin da ‘yan Boko Haram suka kai hari kan tawagarsa.

Kazalika ya yi zargi ne kwanaki kadan bayan an yi ce-ce-ku-ce tsakanin Shugaba Buhari da Majalisar Dattawan kasar, wadda ta bukaci ya sauke manyan hafsoshin tsaron kasar saboda gazawarsu wajen magance rashin tsaron da ke addabar arewa maso gabashin Najeriya.

Masu lura da lamuran tsaro na ganin Shugaba Buhari ya taka muhimmiyar rawa wajen yaki da kungiyar Boko Haram musamman a farko-farkon hawansa mulki a shekarar 2015, inda kungiyar ke rike da garuruwa da dama.

Sai dai suna nuna matukar shakku kan ikirarin da ya sha yi cewa an kwace dukkan yankunan da a baya suke iko da su, suna masu cewa a halin da ake ciki akwai garuruwa da dama da kungiyar ke cin karenta babu babbaka.

Gazawar hafsoshin soji

Bayanan hoto,
Har yanzu akwai jan aiki a gaban manyan hafsan sojin

Galibin ‘yan Najeriya da masu sharhi kan lamarin tsaro da kuma ‘yan majalisun tarayya na da ra’ayin cewa ci gaba da zaman manyan hafsoshin sojin a kan mukamansu na daga cikin manyan abubuwan da suke tarnaki ga yaki da kungiyar Boko Haram.

Masana harkokin tsaro irinsu Barista Bulama Bukarti na da ra’ayin cewa muddun aka bar manyan hafsoshin sojin Najeriya suka ci gaba da rike mukamansu ba zai yiwu a magance matsalar Boko Haram da ta ‘yan bindigar da ke addabar arewa maso yammacin kasar ba.

“A fili take cewa hafsoshin sojin nan da suka shekara biyar sun gaza. Dukkan ‘yan Najeriya bakinsu ya zo daya cewa wadannan hafsoshin soji sun gaza.

“Hatta sojojin da suke karkashinsu wadanda suke yaki a wadannan wurare sun fito sun bayyana yadda shugabanninsu suka gaza. Al’ummar da ake yi don su sun fito sun ce sojojin nan sun gaza, gwamna yanzu ya fito ya yi magana; majalisar kasa har kuduri ta yi na kira ga shugaban kasa ya sauke wadannan hafsoshi amma shugaban kasa ya yi kunnen uwar shegu,” a cewar Barista Bukarti.

Ya kara da cewa ko da yake a baya hafsoshin sun taka rawar gani wajen yunkurin kawar da kungiyar Boko Haram, amma yanzu sun “kwashe shekara biyar suna abu daya ba tare da an magance wadannan matsaloli ba”.

Fadar Shugaban kasa ta sha bayyana cewa bai kamata a sauke hafsoshin tsaro yayin da ake tsaka da yaki ba, sai dai masu lura da lamuran tsaro na ganin rashin isassun kayan aiki da zarge-zargen cin hanci da rashawa suna taka rawa wajen tabarbarewar tsaron, kuma za a kawo karshen hakan ne kawai idan hafsoshin tsaron suka gusa aka samu sabbin jini.

“Akwai zarge-zarge sosai na cin hanci da rashawa musamman a kan manya-manyan sojojin nan. Kananan sojoji sun yi jawabi a boye; sun yi bidiyo sun ce akwai rashin makamai da kuma rashin kula da walwalarsu,” in ji Barista Bukarti.

Wani abu da masu lura da lamura ke gani yana kawo cikas a yaki da Boko Haram shi ne rashin kuzarin da ake zargin Najeriya da nunawa wajen hada gwiwa da sauran kasashen da ke yaki da Boko Haram.

A cewarsu, hakan ne ya sa kwanakin baya Shugaba Idris Derby na Chadi ya yi barazanar janyewa daga gamayyar da ke yaki da Boko Haram a yankin Tafkin Chadi, inda kungiyar ke yawan kai hare-hare.

‘Yan Najeriya da ma masu lura da sha’anin tsaro na zuba ido su gani ko kurar da Gwamna Zulum ya tayar ta zargin sojoji da yin kafar ungulu a yaki da Boko Haram za ta kawo sauyi a game da yadda ake yakin.

Sai dai masana harkokin tsaro sun yi gargadin cewa idan har Shugaba Buhari ya kammala wa’adinsa na biyu kuma na karshe ba tare da shawo kan matsalar ta Boko Haram ba, yankin arewacin kasar zai shiga uku.

More News

Gwamnan Kano ya sanya hannu kan dokar yin gwajin lafiya kafin aure

Gwamnan jihar Kano, Engr Abba Kabir Yusuf ya sanya hannu kan wata doka za ta tilastawa masu yin aure yin wasu gwaje-gwajen lafiya gabanin...

An kashe kwamandan soji a Katsina

An kashe kwamandan sojoji na wani sansanin soji da ke Sabon Garin Dan’Ali a karamar hukumar Danmusa a jihar Katsina a wani harin kwantan...

Magoya bayan APC da dama sun koma NNPP a Kano

Jam'iyar NNPP ta karɓi magoya bayan jam'iyar APC da dama a jihar Kano. Mataimakin gwamnan jihar Kano, Aminu Abdul Salam Gwarzo shi ne ya karɓi...

APC ta dakatar da Ganduje a matakin gunduma

Mambobin jam'iyyar APC a mazabar da ke Karamar Hukumar Dawakin Tofa a Jihar Kano sun dakatar da Shugaban Jam’iyyar APC na kasa Abdullahi Ganduje. ...