Boko Haram: Birtaniya za ta tallafawa wa Najeriya

[ad_1]

UK Prime Minister Theresa May arrived in Nigeria today for her second leg of her three day trip in Africa

Hakkin mallakar hoto
PA

Najeriya ta rattaba hannu kan wata yarjejeniyar tsaro da Birtaniya don taimaka wa Shugaba Muhammadu Buhari yaki da Boko Haram.

An yi shelar wannan yarjejeniyar ne dai a lokacin da Firayim Minister Theres May ta kai ziyara Najeriya.

Wata sanarwa ta ce Birtaniya “za ta fadada tallafin kayan aiki da horaswa ga sojin Najeriya domin kare kansu daga ababen fashewa da ‘yan ta’adda ke danawa”.

Yakin Boko Haram, wanda aka fara a shekarar 2009, ya haddasa mutuwar sama da mutum 20,000 , tare da raba mutum miliyan biyu da gidajensu a arewa maso gabashin Najeriya.

Firayim Ministar ta ce: “Mun jajirce wajen aiki tare da Najeriya domin yaki da ta’addanci da rage tashin hankali, da kuma aza harsashin daidatuwar lamura da kuma arzikin da za su amfane mu gaba daya nan gaba.”

Yarjejeniyar ta kuma kunshi wani sabon shiri na fan miliyan 13 don ilmantar da yara 100,000 wadanda tashin hankali ya katse musu karatu.

Shirin zai samar da kayayyakin karatu da horasa da malamai da kuma wuraren karatu masu tsaro.

Birtaniya za ta kuma taimaka wajen dabarun yaki da ta’addanci da za su taimaka wa Najriya dakile yadda ake samun sabbin mayaka ‘yan ta’adda.

Ga hotunan rattaba hannun a yarjejeniyoyin da aka yi daga fadar shugaban Najeriya:

[ad_2]

More News

EFCC ta musalta cewa Yahaya Bello na tsare a ofishin hukumar

Hukumar EFCC dake yaƙi da masu yiwa tattalin arzikin ƙasa ta'annati ta ce tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello baya ya tsare a hannunta. A...

Mutane 18 sun ƙone ƙurmus a wani hatsarin mota

Aƙalla fasinjoji 18 ne suka ƙone ƙurmus a wani hatsarin mota da ya faru akan babbar hanyar Ojebu-Ode zuwa Ore a yankin Ogbere dake...

AMBALIYA: Bafarawa ya ba wa al’ummar Sokoto gudunmawar naira biliyan 1

Tsohon gwamnan jihar Sokoto, Alhaji Attahiru Bafarawa, ya bayar da gudummawar Naira biliyan daya ga al’ummar Sokoto, domin rage radadin wannan annoba.An bayyana hakan...

Ƴanbindiga sun kai hari coci-coci a Kaduna, sun kuma yi garkuwa da mutane

Mutane 3 ne ake fargabar sun mutu, sannan an yi garkuwa da wasu 30 bayan wani hari da wasu ‘yan bindiga suka kai a...