Kungiyoyin bokaye a Jamhuriyar Nijar sun yi alkawarin amfani da karfin aljannunsu wajen yakar duk wasu kasashen waje da ke yi wa kasarsu zagon kasa.
Wannan bayani ya fito ne a yayin wata ganawa da suka yi da shugaba Janar Abdourahamane Tchiani, wanda aka gudanar a fadar gwamnatin kasar dake Yamai a ranar Alhamis.
A ganawar, an tattauna kan halin da Nijar ke ciki, inda Janar Tchiani ya zargi wasu kasashe da hada kai da Faransa don lalata kasarsa. Daga cikin kasashen da ake zargi har da Najeriya, duk da cewa gwamnatin Najeriya ta musanta wannan zargi.
Bokaye sun yi barazanar daukar mataki, duk da cewa ba su bayyana kasar da ake nufi ba. Shugaba Tchiani ya gode musu bisa irin goyon bayan da suke bai wa gwamnatin soja, yana mai cewa kasarsa na fama da kalubale daga makiya.
A yanzu dai, babu wani martani daga gwamnatin Najeriya ko kuma daga bokaye dake Najeriya kan wannan batu.
Bokayen Nijar Sun Sha Alwashin Yakar Masu Yi wa Kasarsu Zagon Kasa
