Birnin Lisbon zai iya karbar gasar Champions League

Estadio da Luz

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Watakila a yi amfani da filin Benfica mai suna Estadio da Luz wajen buga wasan karshe a gasar Champions League a bana

Watakila birnin Lisbon ya karbi bakuncin wasan karshe na Champions League na bana cikin watan Agusta, idan hukumar kwallon Turai ta amince.

Uefa na shirin dauke wasan karshe na Champions League da ya kamata a buga a Istanbul da aka tsara yi tun 30 ga watan Mayu, wanda aka sake masa fasali.

Haka kuma hukumar na son dauke karawar karshe a Europa League da aka so yi a Poland ranar 27 ga watan Mayu ta mai da shi zuwa Jamus.

Uefa na son buga wasan daf da na kusa da na karshe da na daf da karshe da na karshe a fili daya ba tare da ‘yan kallo ba.

Cikin watan Maris aka dakatar da wasannin cin kofin Zaakarun Turai saboda tsoron yada cutar korona.

Ranar 17 ga watan Yuni ne babban kwamitin amintattu na hukumar kwallon kafar Turai zai yanke hukunci.

Za a buga wasan karshe a gasar Champions League ranar 23 ga watan Agusta, yayin da za a karkare gasar kofin Europa League ranar 21 ga watan na Agusta.

Birnin Lisbon na Portugal yana da manyan filin wasa biyu da dukkan abubuwan da ake bukata wajen buga tamaula da kuma otal da zai dauki kungiyoyin takwas da za su kara a gasar.

An ci gaba da gasar kwallon kafa ta cin kofin Portugal ranar 3 ga watan Yuni an kuma dage dukkan dokar da gwamanti ta saka ta hana zirga-zirga a watannan saboda tsoron yada cutar korona.

Tun ranar 16 ga watan Yuni aka ci gaba da gasar Bundesliga ta Jamus ba ‘yan kallo kuma filin wasa da ke Gelsenkirchen da Cologne da Duisberg da kuma Dusseldorf za su iya karbar bakuncin Europa League.

More News

An ji ƙarar harbe-harbe a fadar Sarkin Kano

A daren ranar litinin ne aka bayar da rahoton jin harbin bindiga a kusa da karamar fadar inda hambararren Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero,...

Ministan shari’a nason INEC ta riƙa shirya zaɓen ƙananan hukumomi

Babban lauyan gwamnatin tarayya kuma ministan shari'a, Lateef Fagbemi ya yi kira da a soke hukumar zaɓen jihohi masu zaman kansu. Da yake magana a...

Kotu ta hana Aminu Ado ayyana kansa a matsayin Sarkin Kano

Babbar Kotun jihar Kano ta hana Aminu Ado Bayero ayyana kansa a  matsayin Sarkin Kano har sai ta kammala sauraron ƙarar dake gabanta. Kotun ta...

NDLEA ta kama wani ɗan kasuwa da ya haɗiye ƙunshi 111 na hodar ibilis  a filin jirgin saman Abuja

Jami'an Hukumar NDLEA dake yaƙi da hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi  sun kama wani mutum mai suna Emmanuel Orjinze wani ɗan kasuwa akan...