Hukumar kula da al’adu, ta Majalisar Dinkin Duniya, UNESCO, ta kada kuri’ar sanya birnin nan mai dimbin tarihi na Babylon ko Babila, wanda ke cikin kasar Iraqi, a matsayin daya daga cikin wuraren tarihi na duniya.
Babylon ko Babila na daya daga cikin fitattun manyan birane na tarihi na zamanin da a duniya, inda ya yi fice wajen al’adu da gine-gine da abubuwa na ban mamaki kamar lambuna dake saman gine-gine.
Babban birnin na Sarki Nabonidus, ya kasance ne a tsakanin kogi mafi tsawo a kudu maso yammacin nahiyar Asiyaa, wanda da ya tashi daga Turkiyya ya kwarara zuwa kudu maso gabashi ya ratsa Syria da Iraqi, wanda ya kasance daya daga cikin biyun da ke samar da ruwa ga Kogin Tigris na Iraqin, a yankin da ya kasance asalin inda ci-gaban duniya ya samo asali.
Birnin Babila, birni ne da ya yi suna a kan kayatattun lambuna da ake yi a sama ko benaye, maimakon na kasa da aka saba gani a wurare, da kuma kofofi masu ban sha’awa ginin gwanaye – kamar Ishtar Gate, wadda tana daya daga cikin abubuwan ban mamaki 7 na ainahi na duniya.
To sai dai a wannan zamani an bata birnin mai dimbin tarihi inda aka jirkita shi daga ainahin yadda ya samo asali ko aka san shi.
An jirkita shi domin gina wa Saddam Hussein fada, sannan kuma su ma sojojin Amurka suka biyo baya da tasu bannar, a lokacin yakin Iraqi, inda ya kasance sansaninsu, bayan da suka kama shi.
Ba wa wuri wannan matsayi na wurin tarihi na hukumar ta kare al’adu ta duniya yana nufin kare shi a matsayin wanda yake da matukar muhimmanci ga dukkanin bil-adama.
An jima ana mamakin yadda wannan birni da ya yi suna wurin abubuwa na ban mamaki nasa bai kasance cikin wuraren na tarihi na hukumar ta duniya ba, tun da farko.