
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya tabbatarwa da yan Najeriya cewa yana ” aiki ba dare ba rana” danshawo kan matsalolin da suka addabi kasarnan.
A sakon sa na Babbar Sallah shugaban kasar ya ce matakan da gwamnatinsa ta dauka kawo yanzu za su “sauya tattalin arziki da kuma kawar da duk wani abu dake hana cigaban kasa.”
Ya kuma shawarci yan Najeriya da su tuna da marasa galihu a lokacin da suke murnar bikin sallah.
A jawabin nasa Tinubu ya kuma ce Najeriya na cikin matsalar tattalin arziki da kuma tsaro amma duk da haka ba matsaloli bane da baza a iya magance su ba.