“Bera nama ne mai kyau kuma yana gyara jiki” — BBC Hausa

Wata mata mai sayar da beraye a kasuwar Ejino da ke a Ikorodu a jihar Legas, ta ce naman bera na da kyau kuma yana gyara jiki.

Shakirat ta ce suna samun naman ne daga mafarauta kuma masu maganin gargajiya ne manyan kostomominsu.

A cewar wani mai maganin gargajiya, suna yi wa masu juna biyu magani ne da naman beran inda suke hada shi da kifi.

Sannan ya kara da cewa shi bai yadda da cutar Lassa ba.

Amma da aka tuntubi wani likitan zamani, ya musanta cewa naman bera na da wani magani.

Ya misalta masu cin naman da masu shan guba da gangan.

More from this stream

Recomended