Tawagar kwallon kafa ta Belgium ta ci gaba da zama ta daya a jerin wadanda ke kan gaba a fagen taka leda a jadawalin da Fifa ta fitar ranar Alhamis.
Mali da Morocco suna daga cikin wadanda suka yi sama a jerin wadanda suka yi fice a kwallon kafa da hukumar kwallon kafa ta duniya, Fifa ta bayyana.
Tawagar Belgium da ta Faransa da Brazil da Ingila da kuma Portugal sun ci gaba da zama a sawun yan gaba-gaba.
Sauran da ke cikin ‘yan 10 farko sun hada da tawagar Spaniya da ta Argentina da Uruguay da Mexico da kuma Italiya, yayin da Jamus ke mataki na 13.
Morocco tana ta 33 a duniya wadda ta taka mataki biyu, bayan da ta lashe Chan a bana, Mali wadda ta yi ta biyu a gasar tana ta 54 a duniya.
Tawagar Uganda da ta Zimbabwe sun ci karo da koma baya zuwa kasa da gubi hudu.
Ranar 8 ga watan Afirilu hukumar kwallon kafa ta duniya Fifa za ta fitar da jerin wadanda ke kan gaba a kwallon kafa a duniya na gaba.
Wadanda ke kan gaba a taka leda a Afirka:
- Senegal
- Tunisia
- Algeria
- Morocco
- Najeriya
- Masar
- Kamaru
- Ghana
- Mali
- Burkina Faso