
Asalin hoton, Getty Images
Hukumar kwallon kafa ta duniya, Fifa ta sanar da nada Anthony Taylor, wanda zai hura wasan karshe a Club World Cup a Morocco ranar Asabar.
Alkain gasar Premier zai gabatar da aikin tare da mataimaka Gary Beswick da kuma Adam Nunn dukkan su daga Ingila.
Ranar Asabar za a buga wasan karshe a gasar kofin duniya ta zakarun nahiyoyi tsakanin Real Madrid da Al Hilal ta Saudi Arabia.
Real Madrid ce mai kofin zakarun Turai Champions League, ita kuwa Al Hilal ita ce ta lashe na zakarun Asia.
Alkalan wasan tamaulan su uku sun yi aiki a gasar kofin duniya da aka yi a Qatar a 2022, wanda Argentina ta lashe na uku jimilla.
Za a buga karawar karshen ranar Asabar a filin wasa na Prince Moulay Abdellah da ke Rabar a Morocco.
Real ta samu gurbin buga wasan karshe, bayan cin Al Ahly ta Masar 4-1 ranar Laraba, ranar Talata Al Hilal ta doke Flamengo ta Brazil 3-2.
Ranar Asabar za a fara wasan neman mataki na uku tsakanin Al Ahly ta Masar da Flamengo ta Brazil.
Jadawalin wasannin Club World Cup:
- Al Ahly da Auckland City (3-0)
- Seattle Sounders da Al Ahly (0-1)
- Wydad Casablanca da Al Hilal (1-1; 3-5 a bugun fenariti)
- Flamengo da Al Hilal (2-3)
- Al Ahly da Real Madrid (1-4)
Wasan neman mataki na uku: 11 ga watan Fabrairu
Wasan karshe: 11 ga watan Fabrairu