Tun gabanin zaɓen fitar da gwani da jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya ne ake raɗe-raɗin cewa akwai ɓaraka a jam’iyyar game da wanda zai tsaya mata takarar shugaban ƙasa, musamman ma wanda shugaban ƙasar Muhammadu Buhari ke mara wa baya.
Sai dai duk da nasarar da Bola Ahmed Tinubu ya samu na kasancewa ɗan takara, lamarin bai mutu ba.
Wasu kalamai da ke fitowa daga bakunan makusantan Bola Tinubu, da shi kansa, da kuma ɓangaren makusantan shugaba Muhammadu Buhari na haifar da tababa kan alaƙar muhimman ɓangarorin biyu da ke da matuƙar tasiri kan nasarar jam’iyyar a babban zaɓen Najeriya na 2023.
Hakan ya ƙara bayyana a fili ne bayan kalaman gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir el-Rufa’i, wanda ya ce “akwai wasu a fadar shugaban ƙasa da ke son ganin ɗan takararmu (APC) ya faɗi zaɓe saboda nasu ɗan takarar bai yi nasara ba.”
Haka nan ma kwanakin baya a lokacin yaƙin neman zaɓen ɗan takarar shugaban ƙasar na APC a garin Calabar, an zarge shi da faɗin wasu kalamai, waɗanda ake ganin tamkar cin fuska ne ga shugaba Muhammadu Buhari.
Kalaman Tinubu da ake ganin tamkar sukar gwamnatin Buhari ne
A baya-bayan nan ɗan takarar shugaban ƙasar na jam’iyyar APC ya yi waɗansu kalamai da ake wa kallon tamkar suka ne ga gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari.
A lokacin yaƙin neman zaɓe a garin Abeokuta na jihar Ogun, Bola Tinubu ya faɗa a cikin harshen yarbanci cewa “koda mai (fetur) zai ci gaba da tsada, su suka san inda suka ɓoye shi, su ci gaba da ɓoye naira, za mu shiga zaɓe kuma za a zaɓe mu.”
“Za ku iya sauya launin naira. Abin da kuke tunani ba zai faru ba. Za mu yi nasara.”
Haka nan a wani gangamin yaƙin neman zaɓen nasa a birnin Calabar na jihar Cross River, Tinubu ya yi wasu kalaman waɗanda ake wa kallon shaguɓe ga shugaban ƙasa Muhammadu Buhari.
Ya ce “sun sa farashin naira ya tashi daga 200 zuwa 800. Inda sun magance wannan matsala ba za mu shiga halin da muke ciki ba a yau, da yanzu mun fi haka.”
“Ba su san hanya ba, ba su iya tunani ba, ba su san yadda ake yi ba.”
Ba da shugaba Buhari nake nufi ba – in ji Tinubu
Sai dai a wata sanarwa da kwamitin yaƙin neman zaɓen Tinubu ya fitar, wadda ta samu sa hannun daraktansa na yaɗa labaru, Bayo Onanuga, kwana ɗaya bayan kalaman na Tinubu a Calabar, ta ce ba shugaba Buhari yake nufi da kalaman nasa ba.
Sanarwar ta ce an yi wa kalaman na Bola Ahmed Tinubu ne gurguwar fassara.
Sanarwar ta ƙara da cewa “kalamin da aka yi kan farashin musayar kuɗi ba an yi shi a kan gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari na jam’iyyar APC ne ba, wani yunƙuri ne na nuna yadda ɓarnar da jam’iyyar PDP ta tafka tun a 2015, lokacin mulkinta, ya kawo matsala a ɓangaren musayar kuɗi na ƙasar.”
Sanarwar ta ƙara da cewa duk wanda ya bibiyi kalaman ɗan takarar shugaban ƙasar na jam’iyyar APC zai fahimci cewar da jam’iyyar PDP yake yi ba da shugaba Buhari ba.
‘Ba a saba ganin irin haka ba’
Dr Abubakar Kari, masanin siyasa, kuma malami a jami’ar Abuja ya ce wannan lamari ne da ba a saba gani ba.
Sai dai ya ce ba abin mamaki ba ne a fagen siyasa.
Ya ce “wannan abu ne ba saban ba, to amma kuma a siyasa babu abin da ba zai iya faruwa ba, siyasa ce.”
Abu ne da ya samo asali
Abubakar Kari ya ce wannan rikici da ke wakana tsakanin Bola Tinubu da wasu makusantan shugaban ƙasa al’amari ne da ya samo asali tun a baya.
Ya ce “lamari ne da ya samo asali tun lokacin da aka kafa gwamnatin shugaba Buhari, magana ce ta gwagwarmayar neman iko da ake samu bayan an kafa gwamnati.”
Ya ƙara da cewa “tun bayan kafa gwamnatin Buhari waɗansu suka ƙeƙashi ƙasa kan cewa ba za su bari Tinubu ya yi kane-kane ba.”
Sai dai masanin siyasar ya ce shi ma Bola Tinubu na da dubaru da ƙwarewa a harkar siyasa, waɗanda yake amfani da su wajen tafiyar da harkar siyasarsa.
Dr Kari ya bayar da misali da cewa lamarin ya fara ƙamari ne tun lokacin zaɓen shugabannin majalisar dokoki jim kaɗan bayan kama mulkin shugaba Muhammadu Buhari a 2015.
Ya ce “a wancan lokacin sun yi bakin ƙoƙarinsu wajen ganin cewar waɗanda Bola Tinubu ya so su zama shugabannin majalisa, wato Ahmed Lawan da Femi Gbajabiamila ba su samu muƙaman ba, inda aka kawo Bukola Saraki da Yakubu Dogara.”
Dr Abubakar Kari ya ƙara da cewa ko a lokacin zaɓen fitar da gwani na ɗan takarar shugaban ƙasa rahotannin sun nuna yadda aka rinƙa ƙulle-ƙulle domin yi wa juna zagon ƙasa a tsakanin ɓangarorin biyu.
Ya ce idan aka lura da irin waɗannan abubuwan da ke faruwa “ni ina ganin akwai ƙamshin gaskiya kan cewar wasu masu faɗa-a-ji da ke kusa da shugaban ƙasa ba su goyon bayan takarar Bola Tinubu.”
‘Haɗari ne ga APC’
Malamin na jam’iar Abuja ya ce wannan rashin jituwa da ake samu tsakanin ɓangarorin biyu na jam’iyyar APC barazana ce ga nasarar jami’iyyar a zaɓe mai zuwa.
Sai dai a cewarsa ba abu ne da za a iya yin hasashe a cikin sauƙi ba.
Ya ce ɓangarorin biyu za su ci gaba da cin dunduniyar juna har sai an samu wanda ya yi nasara.
Ya ƙara da cewa “sai dai hakan babban haɗari ne ga APC domin idan har ɓangarorin biyu suka haɗa kai, to za su fi damar samun nasara a zaɓen da ke tafe.