Bayani Akan Wanda Ya Kamu Da Cutar Korona A Jihar Jigawa – AREWA News

Gwamnatin Jihar Jigawa ta tsinkayi jita-jita dake ta yawo akan an samu ɓullar cutar Korona Bairos a Jihar Jigawa, wanda hakan ke ta yawo musamman a Kafafen Sadarwa.

Duk da cewa hakika wanda ake magana a kansa ɗan asalin Jihar Jigawa ne, amma gwajin da ya tabbatar da cewa yana ɗauke da cutar da sakamakon gwajin ba a gudanar da shi a Jihar Jigawa ba.

Wanda aka samu ɗauke da cutar ya kasance Fasinja ne da ya taso daga Jihar Legas zuwa Jigawa, da shi da ɗan uwansa, inda suka biyo ta Kano, a yayin da suka iso kan iyakar Kano aka tare su, inda Jami’an Yaƙi da Cutar Covid-19 ta Jihar Kano ta killace su, ta kuma gwada lafiyar su, inda daga bisani aka tabbatar ɗaya daga cikin fasinjan na ɗauke da cutar ta covid-19.

Abin takaici da ya janyo hankalin Gwamnatin Jihar Jigawa take ƙarin haske akan wannan batu, shine tuburewa da Gwamnatin Jihar Kano tayi na miƙawa Jihar Jigawa wanda aka samu yana ɗauke da wannan cuta.

Sanin kowa ne, inda da yawa suka yabawa Maigirma Gwamnan Jihar Jigawa, Alhaji Muhammad Badaru Abubakar, tun farko bai yi ƙasa a gwiwa ba wajen tunkarar wannan cuta gadan-gadan ba, inda ya tanadar da matakai da kafa kwamiti da zasu daƙile yaɗuwar wannan annoba a Jihar Jigawa, tare da tabbatar da samar da tallafi domin ragewa al’uma raɗaɗi, hana ma’aikata zuwa wajen aiki, taƙaita zirga-zirga da yin feshi.

A cikin gwamnoni 36 da muke da su a Ƙasar nan, Gwamna Badaru yana cikin sahun farko na gwamnoni da takwarorin sa na Arewa maso Yamma, da suka ɗauki matakin rufe makarantu na kwanaki 30 tun daga 23 ga watan Maris, domin daƙile yaɗuwar cutar.

Duk da haka, idan zamu iya tunawa, Kontirola Janar na Hukumar Shige da Fice na Najeriya Muhammad Babandede, wanda ɗan asalin Jihar Jigawa ne ya kamu da wannan cuta, amma hakan bai sa Birnin Tarayya ko Hukumar NCDC tasa tace Jihar Jigawa nada waɗanda ke ɗauke da wannan cuta ba, don ba a Jihar Jigawa aka yi masa gwaji ba, kuma da sakamakon sa ya fito ba a ce a dawo da shi Jihar Jigawa a killace shi ba.

A dalilin haka ne, Gwamnatin Jihar Jigawa ke ƙara tabbatarwa da duniya cewa, Jihar bata da ko da mutum ɗaya dake ɗauke da wannan cuta a faɗin Jihar a hukumance.

Dagewa da Gwamnatin Jihar Kano tayi na a dawowa Jihar Jigawa da waccan mutumin da aka samu da wannan cutar ne, yasa Gwamna Badaru ya bada umarni Jami’an Ma’aikatar lafiya su tafi Kano su ɗauko mara lafiyan, inda tuni an kawo shi Dutse, inda aka killace shi a wurin da aka tanadar, kuma tuni ya fara karɓan magani.

Jihar Jigawa zata cigaba da bibiya, nuna damuwa da kuma zama cikin shirin dawowa da duk wani ɗan asalin Jihar Jigawa da Allah ya jarrabe shi, a yayin da aka ƙi karɓarsa ko aka ƙyamaceshi a inda yake.

A wannan gaɓar ne, ake kiran jama’a da kar su yarda da wannan labari don a jihar Jigawa ba a samu dlmai ɗauke da wannan cuta ba, kuma har yanzu babu wani wanda ake zargi da wannan cuta.

Gwamna Badaru, yana kuma kira ga al’umar Jihar Jigawa da su ƙara kwantar da hankalin su, kada su tsorata, inda ya ƙara tabbatar musu da cewa zai cigaba da iya ƙoƙarin sa na daƙile yaɗuwar cutar a Jihar Jigawa.

Gwamna Badaru yace Yaƙi akan daƙile cutar Korona Bairos, Yaƙi ne na kowa da kowa, don haka ne ya nemi al’umar Jihar su cigaba da wanke hannayen su akai akai, abi umarnin Ma’aikatar Lafiya, kuma a taƙaita zirga zirga da cigaba da nesanta kai da cuɗanya da mutane.

Auwal D. Sankara (Fica),
(Mataimaki na Musamman ga Maigirma Gwamnan Jihar Jigawa a Sabbin Kafafen Sadarwa)

More from this stream

Recomended