Bayan Goje APC Ta Sake Korar Wani Sanata Da Dan Majalisar Tarayya A Gombe

Jam’iyar APC reshen jihar Gombe to kori sanata mai ci da kuma ɗan majalisar wakilai ta tarayya kan zargin cin amanar jam’iyya a lokacin zaɓukan 2023.

Hakan na zuwa ne kasa da mako biyu bayan da jam’iyar ta kori, Sanata Danjuma Goje shi ma kan zargin cin amanar jam’iyya.

A ranar 8 ga watan Afrilu ne shugabannin jam’iyar na mazabar Bambam suka dakatar da Sanata Bulus K Amos da kuma Yunusa Ahmad Abubakar Mamba mai wakiltar mazabar Yamaltu/Deba a majalisar wakilai ta tarayya.

More from this stream

Recomended