Bauchi: yaro mai shekara 14 ya halaka kansa

Rahotanni da ke fitowa daga jihar Bauchi sun tabbatar da mutuwar wani yaro matashi ɗan shekara 14 da ya halka kansa a Ningi.

Mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar Bauchi Ahmed Wakil ya tabbatar da faruwar al’amarin.

Ya ce yaron ya kashe kansa ne ta hanyar rataye kansa a wani kangon ɗaki.

Mahaifin yaron ne ya sanar da ƴan sanda game da makomar ɗansa. Kuma ya ce yaron yana fama da rashin lafiyar ƙwaƙwalwa.

“Bayan sanar da ƴan sanda nan take jami’anmu suka inda al’amarin ya faru kuma aka ɗauki yaron zuwa babbar asibitin Ningi amma aka tabbatar da ya mutu.”

Rundunar ƴan sandan Bauchi ta ce ta ƙaddamar da bincike domin gano dalilin da ya sa yaron ya kashe kansa.

More News

Hoto:Kwankwaso Ya kaddamar da wasu ayyuka a Kaduna

Biyo bayan gayyatar da gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasiru El-Rufai ya yi masa tsohon gwamnan jihar Kano, Rabi'u Musa Kwankwaso ya kaddamar da wasu...

Sarkin Kano Aminu Ado ya zama uba ga Jami’ar Calabar

Mai martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya samu girmamawa bayan an nada shi a matsayin uban Jami'ar Calabar da ke Jihar Cross...

Za a yi Ruwan Sama a Wasu Garuruwan Adamawa —Mai hasashe

Wani mai hasashen yanayi a Najeriya Alhaji Adamu Katakore ya faɗa cewa za yau Alhamis za a samu ruwan sama a wasu garuruwan jihar...