Wasu daga cikin masu amfani da layukan sadarwa a babban birnin tarayya Abuja sun nuna damuwa kan yadda kamfanonin sadarwa ke kara farashin data da kati ba tare da inganta ayyukansu ba.
A cikin hirarraki daban-daban da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ta yi da su, masu amfani da layin waya sun bayyana cewa duk da karin kudin da kamfanoni ke yi, sadarwa ta ci gaba da zama babu kyau.
A wani jawabi da ya fitar a ranar 6 ga Fabrairu, 2024, Babban Mataimakin Shugaban Hukumar Sadarwa ta Najeriya (NCC), Dr Aminu Maida, ya ce za su rika daukar mataki kan kamfanonin da ke bada sabis mara inganci.
Wani daga cikin masu amfani da layin sadarwa, Ogah Paul, ya ce yana da isasshiyar data amma ba ya iya amfani da ita saboda matsalolin sadarwa.
Ya ce yana mamakin ko ma’aikatan kamfanonin sadarwar su na iya amfani da irin wannan sabis din da suke baiwa mutane.
Sai dai wata mata mai suna Josephine Tanko ta ce ba ta da matsala da kamfanin sadarwar da take amfani da shi.
“Basu iya komai sai shan data” – Masu amfani da layukan waya sun koka kan karin kudin data da raunin sabis
