Bashir Dandago: Genevieve ta yi mini kyautar da ba zan manta da ita ba

Bashir Dandago: Genevieve ta yi mini kyautar da ba zan manta da ita ba

Bashir Dandago ya ce abin da ya faru dangane da wakar Fadimatu uwar Sharifai wanda ba zai taba mantawa da shi ba shi ne, bayan kyautuka da ya samu na alkhairai kamar kujerun Makka inda masoya Manzon Allah suka ba shi kujeru ya kai ziyara, to abin da ya fi ba shi mamaki shi ne, yadda wanda ba Musulmi ba ya masa kyautar da ya ji dadinta.

Sha’irin ya ce,” Na je Legas wani taro, a nan ne na samu ganawa da daya daga cikin fitattun ‘yan wasan Nollywwod wato Genevieve Nnaji, inda a take ta yi mini wata dunkulalliyar kyauta wadda ba sai na fada na ce kaza ba ne to amma na san wannan kudin a lokacin za su kai ni Makka”.

Ya ce, ” A lokacin na yi waka sai Genevieve ta yi mamakin cewa ya aka yi kamar ni ba ni da mota, sai na ce mata ai abubuwa muke na addini, to a gaskiya na ji dadin wannan kyautar da ta yi mini”.

Mawakin ya ce abin da ya sa ta yi mini wannan kyautar saboda tana jin wakokina sai ga shi kuma ta ganni ido da ido har ta ji ni ina yin wannan waka da take so.

Tarihin Bashir Dandago

An haife shi a a shekarar 1966 a unguwar Dandago a cikin birnin Kano a wani gida babba da ake kira Gidan Rafi, wanda a yanzu haka akwai mutum sama da dubu a cikinsa.

Shekarunsa a 2021, 56, ya yi makarantar firamare a Dandago, daga nan ya wuce zuwa makarantar koyon kasuwanci ta Aminu Kano Commercial College, da ke Goron Dutse, inda a nan ya kammala sakandire.

Bayan kammala sakandire ya wuce zuwa FCE Kano, inda ya yi Diploma a fannin kula da harkokin Jama’a, wato Public Administration a Ingilishi.

Ko yaushe ya fara waka?

Bashir Dandago ya ce, batun yabon Manzon Allah (SAW), tun suna kanana suka tashi a cikinsa, saboda sun tashi sun ga iyayensu na yi.

Ya ce a harkar da ta shafi majalisi, akwai kungiyar da ta raine shi ita ce Kursha’ul Nabiyi, wadda ita ce kungiya ta farko a Najeriya a bangaren majalisi.

Ya kansace shi dan kungiyar ne suna wake-wake iri daban-daban, don haka tun yana karami yake wake-wake.

Ya ce ya yi wakoki da dama, amma wadda aka fi saninsa da ita ita ce ta ‘Fadimatu Uwar Sharifai.’

Bashir Dandago ya ce saboda ficen da wakar ta uwar Sharifai ta yi an zaci ko ita ce wakarsa ta farko, to amma kafin ita ya yi wakoki sama da 300.

Sha’irin, ya ce wakar ”Fadimatu Uwar Sharifai” na da baiwar da yayinta ba ya karewa saboda sonta da jama’a ke yi.

Ya ce, ” Duk inda na je idan ban yi ba sai a ga kamar ma ban je taron ba”.

Dalilin da ya sa nayi wakar Uwar Sharifai

Bashir Dandago ya ce, kauna ce ga ahalin Manzon Allah (SAW), sun tashi a kan kaunar gidan sun kuma sanya wa ‘ya’yansu ma wannan kaunar shi ya sa ya yi wakar.

Mawakin ya ce, akwai wasu wakokinsa da suka yi fice bayan ta Uwar Sharifai, kamar wakar ‘Zama da kishiya’, saboda yadda mata ba sa son zama da kishiya shi ya sa ya yi wakar inda ya fadi yadda ake zama da kishiya.

Sha’irin ya ce,” A yanzu haka ina da mata uku da ‘ya’ya 25 masu rai, na kuma binne 5, sai jikoki 7.

Ya ce akwai ‘ya’yana da suka gaje ni, don akwai É—ana da tun yana shekara uku ya fara waka.

Wakar da ya fi so ya ce ita ce ta ‘Armashin ado’, don ya fi daukarta a matsayin bakandamiyarsa.

Bashir Dandago ya ce, bayan wakokin yabon Manzon Allah (SAW), idan mutum ya burge shi ma yakan masa waka, kamar Sarkin Kano Alhaji Ado Bayero, ya masa waka.

Ya ce, sarkin Kano na yanzu Alh Aminu Ado Bayero ma ya masa waka, haka amininsa Aminu Ladan da aka fi sani da Alan waka ma ya masa waka.

Bashir Dandago ya ce a cikin halayyarsa ba shi da riko, wannan hali nasa ya sa ya samu matsala tare da abokinsa na harkar yabo wato Sharu Rabi’u san Baba.

Ya ce saboda duk abin da aka yi mini in dai ban ji dadinsa ba sai na fada wa mutum, don duk abin da ya yi na kuskure sai na tunkare shi na fada masa har ma masoyansa suka rinka ganin kamar ni makiyinsa ne in ji shi.

Mawakin ya ce baya ga waka, yana wasu sana’oi da yake yi na neman abinci, sannan ya yi aiki da kafafen yada labarai da dama inda a yanzu haka yake tare da Liberty Radio a Kano.

Menene burinsa?

Sha’irin ya ce babban fatansa shi ne ya yi ta ziyarar Annabi Muhammad (SAW), sannan kuma yana so ya mutu a ranar Jumma’a domin mahaifiyarsa da mahaifinsa duk a ranar Jumma’a suka mutu.

More News

Qatar za ta taimaki marayu a Najeriya

Gwamnatin kasar Qatar ta bayyana cewa za ta ba da tallafi ga yara marayu sama da 1,000 da suka rasa iyayensu saboda rikicin Boko...

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma’aikatar kudin jihar ta miĆ™ata bayanan bashin da El-Rufai ya ciwo

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma'aikatar kudi ta jihar da ta miƙa mata cikakken bayani kan basukan  da gwamnatin tsohon gwamnan jihar, Nasiru...

An dakatar da ayyukan kamfanin jiragen sama na Dana Air

Festus Keyamo, ministan harkokin sufurin jiragen sama ya umarci hukumar FAAN dake lura da sufurin jiragen sama a Najeriya ta dakatar da ayyukan kamfanin...

Yahaya Bello Ya Bayyana Dalilan Da Ya Hana Shi Bayyana A Gaban Kotu

Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya ce tsoron kamun  hukumar EFCC dake yaĆ™i da yiwa tattalin arzikin Ć™asa ne ya hana shi bayyana...