
Hakkin mallakar hoto
Getty Images
Barcelona tana ta daya a teburin La Liga da tazarar maki biyu tsakaninta da Real Madrid
Ranar Laraba Barcelona za ta gwada ‘yan wasanta cutar korona a lokacin atisaye, a shirin da ake yi na ci gaba da gasar La Liga ta 2019-20.
A wannan makon aka bai wa kungiyoyin Spaniya damar fara atisaye, bayan da gwamnatin Spaniya ke shirin cire dokar hana zirga-zirga.
- ‘Yan Barcelona sun rage albashi saboda coronavirus
- Ana ta tsara yadda ‘yan wasan La Liga za su koma atisaye
Barcelona ta ce mahukuntan gasar La Liga sun amince ta yi gwajin a filin atisayenta, bayan da aka amince da kayayyakin aikin da ta tanada.
Mahukuntan gasar La Liga na fatan ci gaba da wasannin bana cikin watan Yuni da zarar gwamnati ta amince.
An amince ‘yan wasa su yi atisaye a matakin daidaiku kafin su yi cikin rukuni duk don gudun yada cutar korona.
Cikin watan Maris aka dakatar da gasar La Liga, bayan da cutar ta bulla a Spaniya, amma sai an gwada ‘yan wasa kafin a koma ci gaba da wasannin bana.
Saura wasa 11 a karkare gasar La Liga ta bana, kuma Barcelona ce ta daya a kan teburi da tazarar maki biyu tsakaninta da Real Madrid.